Labarai

Ba Mu da Isassun Takardun Buga Sababbin kudade – Emefiele

Ba Mu da Isassun Takardun Buga Sababbin kudade – Emefiele .

Gwaman Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce bankin ba shi da isassun takardun da zai ishe shi buga sababbin kuɗin da ake buƙata a ƙasar.

Mista Emefiele ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da yake gabatar da jawabi ga taron majalisar magabata ta ƙasar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasar, kamar yadda wata majiya ta shaida wa Jaridar MANUNIYA a ƙasar.

Gwamnan Babban Bankin ya shaida wa majalisar magabatan cewa hukumar da ke lura da buga takardun kuɗin ƙasar ba ta da isassun takardun buga sababbin kuɗin, abin da ya sa aka kasa buga wadatattun takardun kuɗi da aka sabunta a ƙasar.

Hukumar ba ta da takardun da za ta buga 500 da 1,000. Amma sun yi odar takardar daga ƙasashen Jamus da Birtaniya, to sai dai har yanzu layi bai zo kansu ba kasancewar akwai layi a odar, dan haka odarsu ba za ta samu yanzu ba”, in ji Emefiele.

Ya ƙara da cewa “CBN ya buƙaci hukumar da ke buga kuɗin da ta buga kofin takardu miliyan 70, abin da zai isa a buga naira biliyan 126 da za a sake su, su zagaya hannun mutane a wannan rana ta Juma’a, to amma hukumar ba ta da isassun takardun da za ta yi wannan aiki”. Kamar yadda majiyar ta shaida wa jaridar MANUNIYA.

A makon da ya gabata ne dai shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya alƙawarta cewa za a shawo kan matsalar cikin kwana bakwai.

Tuni dai wasu jihohin ƙasar sun shigar da ƙarar gwamnatin tarayya da Babban Bankin domin ƙara wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar.

Lamarin da ya sa Kotun Ƙolin ƙasar ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗin har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairun da muke ciki, lokacin da za ta yanke hukunci kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button