PDP Ta Kori Chimaroke Nnamani, Da Wasu 6 Na Cikin Ta
Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP ya kori tsohon gwamnan jihar Enugu, Sanata Chimaroke Nnamani da wasu mutane 6 bisa zargin cin zarafin jam’iyyar.
Ku tuna cewa a watan jiya ne jam’iyyar ta dakatar da Sanata Nnamani.
Jam’iyyar PDP NWC a karshen taronta na 566 ta bayyana hakan a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar.
A cewar sanarwar, jam’iyyar ta amince da korar ta ne sakamakon wasu munanan laifuka da suka saba wa kundin tsarin mulkin PDP (kamar yadda aka yi wa gyara a shekarar 2017).
Sauran da aka kora daga Jam’iyyar sun hada da:
Hon. Chris Ogbu (Jihar Imo), Ajijola Lateef Oladimeji (Ekiti Central), Olayinka James Olalere (Ekiti Central II), Fayose Oluwajomiloju John (Ekiti Central I), Akerele Oluyinka (Ekiti North I) da Emiola Adenike Jennifer (Ekiti South II). .
Sanarwar ta kara da cewa “korar ta fara aiki ne daga yau Juma’a, 10 ga Fabrairu, 2023.
“Shawarar ta NWC ta biyo bayan shawarar kwamitin ladabtarwa na kasa da kuma bin sashe na 58 da 59 (1) (g) na kundin tsarin mulkin PDP (kamar yadda aka gyara a 2017).
Jam’iyyar PDP ta bukaci daukacin ‘ya’yan jam’iyyar mu da ke fadin kasar nan da su ci gaba da kasancewa da hadin kai tare da mai da hankali kan manufofin jam’iyyarmu na Ceto da sake ginawa da kuma karkatar da al’ummarmu daga rashin mulki”.