Siyasa

KANO: APC Ta Gargadi NNPP Kan Ta Shiga Taitayin Ta

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta yi gargadin cewa idan har jami’an tsaro ba su dau mataki na dakatar da kai hare-hare na rashin hankali da kuma barnata kayayyakin yakin neman zabenta da jam’iyyar adawa ta NNPP ke yi ba, jam’iyya mai mulki ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen baiwa mambobinta karun nasara ba.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben Gawuna/Garo, kuma kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano, ya ce duk wani hari da aka kai kan mambobin jam’iyyar APC ko magoya bayan jam’iyyar APC, za a gamu da matakan da doka ta tanada.

Ya ce ya kamata jam’iyyar NNPP ta kira ‘ya’yanta don basu umarnin su tsaya a kan turbar zaman lafiya, idan ba haka ba su gane cewa tashin hankali ba shi ne mafita ga kowace jam’iyya dake jin kanshin nasara ba.

Malam Garba ya ce Kano ta samu zaman lafiya a ‘yan kwanakin nan, kuma jam’iyyar APC ta jajirce wajen gudanar da yakin neman zabe cikin lumana tare da yin aiki dare da rana domin ganin an samu nasara a zaben, wanda ‘yan adawa ke fargabar hakan.

Kwamishinan ya yi nuni da cewa, abin takaici ne yadda jam’iyyar NNPP da ba ta ji dadin dimbin goyon bayan da APC ke samu daga al’ummar jihar ba, yanzu ta fara tayar da zaune tsaye domin nuna bacin ransu.

Ya ci gaba da cewa yayin da jam’iyyar NNPP ke tayar da jijiyar wuya ga jam’iyyar APC, shugabanta Haruna Doguwa, a kokarinsa na boye wannan ta’asa yana kukan wasu korafe korafe na daban.

Malam Garba ya ce jam’iyyar APC ta tattara hujjoji kan abubuwan da bata garin jam’iyyar NNPP suke yi da suka hada da kashe-kashe, cutar da jiki, lalata tambari da kayayyakin yakin neman zabe.

Kwamishinan ya yi tir da cewa shirun da jam’iyyar NNPP ta yi kan hare-haren da ake kai wa jam’iyyar APC, ya tabbatar da ba wai kawai goyon bayansu ga tashe-tashen hankula ba ne, har ma da shirin tada zaune tsaye, da kuma shirin tayar da tarzoma domin a tsoratar da jama’a da kada su fito su yi amfani da ‘yancinsu wajen zaben shugabannin da suke fatan su kasance wakilansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button