Labarai

Shugaban Kasar Rasha Yayi Alƙawarin Tallafa Wa Mali Wurin Yaƙar Masu Iƙirarin Jihadi

Shugaban Kasar Rasha Yayi Alƙawarin Tallafa Wa Mali Wurin Yaƙar Masu Iƙirarin Jihadi..

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya alƙawarta ci gaba da tallafa wa gwamnatin mulkin sojin Mali, wadda ke fama da tashe-tashen hankulan masu iƙirarin jihadi tun 2012.

A shekarar da ta gabata Mali ta juya wa tsohuwar uwar gijiyarta wato ƙasar Faransa, baya, inda ta juya akalar neman tallafi zuwa Rasha.

Wannan dai ita ce ziyarar Mista Lavrov ta biyu zuwa nahiyar Afirka cikin makonni biyu.

Rasha na buƙatar tallafa wa sabbin ƙawaye a yayin da yaƙin da take yi a Ukraine ke ci gaba da zafafa, to sai dai dangantakarta da ƙasashen yammacin Afirka ta daɗe da yauƙaƙa.

Misat Lavrov, wanda ke ziyarar kwana biyu a Mali ya bayyana aniyar ƙasarsa ta son bayar da tallafin soji ga gwamnatocin ƙasashen yammacin Afirka domin yaƙar ayyukan masu iƙirarin jihadi.

Gwamnatin mulkin sojin Malin ta yi watsi da sukar da ake yi mata game da mayar da hankali wajen ƙulla alaƙa da ƙasar Rasha.

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya ce ”ba dole ne sai mun yi wa mutane bayani idan za mu ƙulla alaƙa da wani ba. Rasha ta zo ƙasarmu ne bisa bukatar tallafinta da muka yi.

Kusan fiye da shekara guda ke nan tun bayan da ƙungiyar sojojin hayar Rasha ta Wagner ta fara aiki a ƙasar Mali, duk da cewa hukumomi ba su tabbatar da batun a hukumace ba.

To amma hujjoji na nuna cewa ba su taɓuka wani abin a zo a gani ba, wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadin, kuma matsalar rashin tsaron na ci gaba da munana.

Wasu alƙaluma daga cibiyar tattatara bayanai kan rikice-rikice ta ‘Acled Info’ sun nuna cewa an samu ƙaruwar fararen hular da rikice-rikicen ya shafa fiye da ruɓin adadin da aka samu kafin zawan su.

To sai dai duk da wancan iƙirari na ƙungiyar ‘Acled Info’ gwamnatin mulkin sojin Mali ta yi watsi da rahotonnin da ke cewa yanayin tsaron ƙasar na ƙara taɓarɓarewa, tana mai cewa labarai ne na ‘ƙanzon kuruge.

Domin haka ta haɗa gwiwa da Rasha wajen tallafa wa dakarun sojin ƙasar.

Lamarin da ya sa Rashar ta kai manyan kayan aikin soji zuwa Mali a lokuta mabambanta tun bayan da sojoji suka karɓi mulkin ƙasar a watan Agustan 2020.

Kayan sojin da Rasha ta kai sun haɗa da jiragen yaƙi, tare da jirage masu saukar ungulu.

A shekarar da ta gabata masu zanga-zanga a Mali sun nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin

Shugaban mulkin sojin ƙasar Kanal Assimi Goïta ya ce nasarar da muka samu ta fuskar yaƙi da ta’adanci a cikin shekara biyu ya zarta ci gaban da muka samu na shekara 10 da suka gabata.

Makamanmu sun zama abin alfaharinmu, in ji Kanar Goïta a wani jawabi da ya gabatar a bikin ranar sojin ƙasar cikin watan da ya gabata.

Ya ƙara da cewa mutane na ci gaba da komawa gidajensu, to sai dai bai bayar da misali ba.

Bayyanar sojojin hayar Rasha a ƙasar ya kawo cikas ga ƙoƙarin Faransa da ƙawayenta na taimaka wa Mali fatattakar ‘yan tawayen da suka shafe kusan shekara 10 suna addabar ƙasar.

Zuwan dakarun wagner na zuwa ne bayan da dakarun Faransa suka fara raguwa a ƙasar, waɗanda suka kawo gagarumin sauyi wajen yaƙar ‘yan tawayen a farkon zuwansu a shekarar 2013.

Kafin zuwa sojojin Wagner yawan dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a ƙasar ta MINUSMA ya kai 18,000.

To sai dai dakarun sun fara samun cikas ne bayan da ƙasashen Jamus da Birtaniya da Ivory Coast da Benin suka bayyana janye dakarunsu kuan 3,000.

Hare-haren ressan ƙungiyar ISIS da al-Qaeda sun yi ta yaɗuwa zuwa makwabtan ƙasashen Burkina Faso da Nijar, yayin da ayyukan masu tayar da ƙayar baya ke faɗada zuwa yankin tekun Guinea.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu