Siyasa

Bola Tinubu Ya Gana Da Wasu Malaman Addinin Musulunci A Katsina

Bola Tinubu Ya Gana Da Wasu Malaman Addinin Musulunci A Katsina.

Dan takarar shugaban kasar tarayyar Najeriya karkashin tutar jam’iyyar APC, Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya yi zama na musamman tare da shugabannin addinin musulunci na jihar Katsina a lokacin da ya ziyarci jihar Katsina cikin daren ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu 2023.

Taron ya gudana ne a babban dakin taro na gwamnatin jihar Katsina wanda ya samu rakiyar Gwamnanonin jihohin Katsina, Zamfara, Jigawa, Kebbi, Sanata Abu Ibrahim, Sanata Hadi Sirika, Rt. Hon. Tasiu Zango, Dan takarar gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar APC, Dakta Dikko Radda, mataimakin sa, Hon. Faruq Lawal Jobe, Sanata Bello Mandiya, Alh. Nuhu Ribadu, Alh. Ibrahim Masari, da sauran su.

Sheikh Hadi Balarabe a madadin darikar Tijjaniya, yayi ma Dan takarar shugaban kasa barka da zuwa jihar Katsina tare dayi mashi fatan alkhairi da samun nasara a zaben 2023.

Ya bada tabbacin cikakken gowon bayan su a madadin darikar Tijjaniya na jihar Katsina da kuma mutanen da suke da alfarmar su.

Wakilin Kungiyar Ahlul sunnah, ya bayyana gamsuwar su kan takarar Ahmed Tinubu da Kashim Shattima a matsayin mutanen da zasu kawo cigaba ga addinin musulunci da kasar Najeriya bakin daya.

A karshe ya bayyana cewa sun hada kai domin bashi gudunmuwa Don ganin ya cimma burin shi na zama shugaban kasar Najeriya.

Shima Dan takarar gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar APC, Dr. Dikko Radda, ya bayyana godiyar shi ga malaman jihar Katsina bisa ga irin goyon baya da suka ba Gwamna Aminu Bello Masari wanda a cewar shi, ya kare hakkunan addinin musulunci.

Ya bayyana irin gagarumar gudunmuwa da malaman addini zasu bada wajen zaben shugaba nagari, sannan yayi kira gare su da su kalli dukkanin yan takarar shugaban kasa suyi masu alkalanci da ayyukan da sukayi a baya.

Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya bayyana Ahmed Tinubu a matsayin mutum mai kishin Arewa tun a lokacin marigayi Shehu Musa Yaradua. Ya bayyana shi a matsayin mutumen kirki wanda yayi abun kirki a lokacin da yake gwamnan jihar Lagos wanda har yanzu bisa turbar shi jihar ke tafiya.

Ya roki alfarmar malaman da su zabi Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya domin kawo cigaba.

Da yake maida martani, Ahmed Bola Tinubu, ya shaida cewa babu abun da zai ce sai godiya ga irin karramawa da karamchi da Al’ummar jihar Katsina suka nuna mashi.

Yayi godiya ta musamman ga irin gudunmuwar da Gwamna Aminu Bello Masari ya bashi tun lokacin da zai tsaya takarar shugaban kasa wanda yake alfahari da mutanen jihar Katsina. Ya gode ma malamai da irin kyawawan fatan alkhairi da suke yi mashi tare da basu tabbacin cewa zai rike amanar addinin musulunci da al’ummar Najeriya baki daya.

Daga karshe ya mika sakon jaje da alhini ga al’ummar da suka rasa rayukan su ta hanyar yan ta’adda a Bakori da sauran sassan jihar Katsina. Ya kuma bada gudunmuwar Naira miliyan Dari (N100,000,000) ga al’ummar da wannan ibtila’i ya fadamawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button