Magunguna

Yadda Za’ayi Maganin Amosanin Ka

Amosanin ka wata cuta ce dakan fito akan mutum mace ko namiji kuma yakan sanya kan mutum yayi fari harma ya dinga fitar da wani farin gari akan mace ko namiji.

Amosanin ka idan har yay yawa yakan gangaro ido, yakansa idon mutum ya diga ruwa kokuma ido yayi ja kai wani idan yay yawa matuka kansa yasa mutum ya dinga gani dishi dishi buguda kari yakan sanya yawan mantuwa.

Don kula da lafiyar jikinku Insha Allah zamu kawo muku magnin wannan cuta ta amosanin Ka.

ABUBUWAN DA ZAKA NEMA.

• Ganyen Magarya.

• Man Zaitun.

YADDA ZAKA SARRAFA WADANNAN ABUBUWA.

Da farko zaku samu ganyen magarya dinku mai kyau saiku shanya shi ya bushe, Bayan ya bushe saiku daka shi ya daku sosai.

Saiku Samu tukunya dinku kukawo ruwa kamar kofi 4 ko biyar saiku zuba a cikin wannan tukunya. Saiku kawo garin magarya din nan saiku zuba Cokali biyu.

Saiku dora akan wuta ku tafasa shi sosai, bayan kun tabbayar ya tafasu saiku sauke shi, abarshi ya huce sosai.

Bayan ya huce sai a wanke kai dashi sosai mace ko namiji, bayan an wanke sai a barshi ya bushe sosai.

Sai a kawo wannan Man Zaitun sai a shafe kai dashi ko ina idan macece ta goga lokoda sako na cikin gashin kanta.

ABIN LURA:

A tabbatar an tace ruwan kafin a fara wanke kan dashi.

Kuma za’ayi tayin haka har na tsawon sati daya ko biyu.

Akarshe muna aduar Allah yabada lafiya gamasu wannan cuta Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu