Cikakken Tarihin Ali Jita
Ali Isah Jibrin Haihuwa: 5 Yulin shekarar 1983) Ana masa laƙabi da Ali Jita a fannin waƙa, ana kuma kiran shi da Mai jita ko Ali Isah Jita sunan shi na yanka shine Ali Isah Jibrin, Ya kasance mawaƙin Hausa na zamani, marubucin waƙa kuma mai rerawa.
An haife shi a jihar Kano a wani gari mai suna Gyadi gyadi, Ali jita ya tashi a Shagari quarters a ƙaramar hukumar Kumbotso.Daga bisani kuma aiki ya mai da mahafinsu da su garin Lagos daga baya suka ƙara komawa Abuja.
Sunan mahaifinsa Alhaji Sallau Jibrin Kibiya ya kasance mahauci ne, Mahaifiyarsa kuma Hajiya Ummul-Khairi.
Karatu
Ali jita ya fara karatun noziri a shagari quaters, yayi karatun firamari da sakandari a Victoria ireland dake Lagos a cikin wani barikin sojoji mai suna bonikam barrack, ya karasa karatun sa na sakandiri ne a Abuja.
sannan ya zurfafa karatunsa a Federal college of education kano inda ya karanta Public administraion, inda aka bashi darajan shaidawa ta National Diploma, sannan kuma ya karan ta ilimin kwamputa a Intersystem ICT School inda ya kara samun shaida na Diploma.
Waka da fim
Yawancin wakokin Ali jita an saka su a masana’antar fim ta Kannywood, Amman wasu daga cikin Albom din shi kuma an sayar dasu ne a wajen Kannywood, Yana waka ne tare da shahararren mawaki Nazifi Asnanic da kuma Fati Nijar a matsayin abokan arziki.
harwa yau, shahararren mawakin yayi waka tare da Nazir M Ahmad mai suna Mama, sannan yayi waka tare da Umar M Shareef mai suna Kano.
A shekaran 2018, Ali jita yayi wata waka mai suna Love, wakar ta lashe lambar girma na jadawalin wakokin da suka fi kowanne a shekaran, a inda wakan tazo na biyu, kamar yanda BBC Hausa suka dauko rahoto.
Ali jita yayi amfani da salan Ingausa wajen rubuta wakan da kuma rerawa. A shekaran 2019, yayi bidiyon wakan sa mai suna Arewa angel tare da tsohuwar jaruman Kannywood mai suna Rahama Sadau.
Rayuwa
Ali jita ya fara harkan waka tin yana dan shekara 16 a lokacin yana makarantan islamiyya a Lago tin lokacin da yake zurfafa karatun sa a Federal college of education kano ya kasance yana dan taba waka kadan-kadan.
haka ya cigaba da taba waka har girman sa. ya kasance mutum ne mai saukin kai, yana da sanyayyar murya. Mutum ne kuma mai yawan murmushi.
Yana san Nazifi Asnanic a matsayin abokin kirki a wajen waka da kuma cikinta.
Kuma su biyun makusantan juna ne a harkan waka, sunyi wakoki dayawa tare irinsu Aboki da Ruwan zuma. An kira shi da Ali jita ne saboda san jita da yakeyi, kuma yana yawan rike Jita a wakokinsa da kuma ambatan sunanta.
Ali jita yana da aure harda yara biyar, Usman suna kiranshi da Affan, da Aliyu inkiya Ramadan, Ahmad farid, zainab hidda sai Aisha ana kiranta da Afra.
Kundin Wakoki
Albom Wakoki Shekara Adadin wakoki
Labarin duniya wacece nake so
Labarin duniya
Bakandamiya 3
Murmushin alkawari
Zaman gida
Buje Remix
Uwar gida
Labarin jita remix
Rayuwa
Chan changi
Ga amarya ga ango remix
So sinadari remix
Zakin maza *Rabbana
*Duniya
*watan Azumi
*Farar diya
2016
Mata *Mata 2018
Arewa Angel
Mamana
Tarkon kauna
Gimbiyar mata
Buri uku
Yar lele
Duniya
Halimatu sadiya
Asha ruwa
Jawabi
Yara yara
Kece
Love
Indo
Aure
Zaman aure
Farar diya
Zakka
Mai jita
Fati fati
Kano