INEC Ta Bayyana Tinubu A Matsayin Wanda Yayi Nasara A Jihar Jigawa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a jihar Jigawa a ranar Asabar da ta gabata.
A cewar jami’in tattara bayanan, Farfesa Arma Ya’u Hamisu Bichi, a ranar Litinin, Tinubu ya samu kuri’u mafi yawa a zaben da ya gabata a jihar.
Da yake bayyana sakamakon zaben shugaban kasa, Bichi ya ce Tinubu ya samu kuri’u 421,390, yayin da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 386,587.
Bichi ya kara da cewa Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya samu kuri’u 98,234 yayin da Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP) ya samu kuri’u 1,889.
Kujerun Sanatan Jigawa
Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe kujerun ‘yan majalisar dattawa guda biyu, da na ‘yan majalisar wakilai takwas yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ta lashe kujerun majalisar dattawa daya, da wakilai biyu, ita kuma NNPP ta lashe kujerun majalisar wakilai daya.
Alhaji Mustapha Khabib na PDP ya lashe zaben JIgawa Kudu maso Yamma da kuri’u 153,73.
Dan takarar jam’iyyar APC Alhaji Babangida Husaini ya lashe zaben kujerar sanatan JIGAwa na arewa maso yamma da kuri’u 187,049 sai kuma Ambasada Abdulhamid Ahmed Malammadori ya lashe zaben kujerar sanatan arewa maso gabas na JIGAwa da kuri’u 136,977.