Labarai

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 2 Hukunci Kisa Kan Kashe Ma’aurata A Ondo

Wata babbar kotun Jihar Ondo da ke zamanta a Akure babban birnin jihar, ta yanke wa wasu mutum biyu Ayuba Idris da Tasur Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kama su da laifin kisan kai da fashi da makami.

An gurfanar da wadanda aka yanke wa hukuncin ne bisa laifin kisan ma’aurata, Mista Kwaku Richard Kwakye da matarsa Misis Tope Kwakye.

Lauyan jiha, John Dada shi ne ya garfanar da Idris da Abubakar a gaban kotun bisa tuhume-tuhume guda biyar.

Tuhume-tuhumen da aka karanto ga wadanda aka yanke wa hukuncin na fashi da makami ga ma’aurata Mista da Misis Kwalle gami da kashesu a ranar 1 ga watan Mayun 2019 wajajen karfe 8:30 na dare a rukunin gidajen Ojomo Akintan da ke Olufoam a garin na Akure.

Laifukan da ake zargin mutum biyun ya saba wa sashi na 6(b),(1,2)(a)&(b),324,319, 319(1) na dokar fashi da makami, Cap 11, Volume 14, na dokar tarayyar Nijeriya, 2004.

Tun da fari dai Dada ya shaida wa kotun cewa wadanda aka kama da laifin sun yi fashi ga ma’auratan ne dauke da muggan makamai inda suka kashesu da kebur din mashin bayan musu fashin.

Da ya ke yanke hukunci kan shari’ar, Mai shari’a Williams Olamide, ya ce, mai shigar da kara ya gaza gabatar da kwararan hujjoji kan tuhume-tuhume na farko da na biyu kan wadanda ake zargin.

Kan hakan Olamide, ya yi fatali da kara na daya da na biyu.

Sannan, alkalin ya kama wadanda ake zargi da laifi kan tuhumar da ake musu na uku da ya yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai.

A sauran tuhume-tuhumen kuma alkalin ya yanke wa wandada ake kara hukuncin kisa ta rataya har sai sun mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button