Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Aisha Aliyu Tsamiya

Aisha Aliyu Tsamiya (an haife ta a shekara ta 1992) a ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar Kano a Arewacin Nijeriya. A halin yanzu tana karatu ne a Jami’ar Yusuf Maitama Sule dake a jihar Kano.

Tarihi

Aisha Aliyu, wata matashiyar ƴar fim din hausace da take da burin zama babba a harkar fim. An haifeta a ƙaramar hukumar Nasarawa dake jihar Kano. Ta tafi makarantar firamare da sakandare ta Giginyu kuma a halin yanzu tana neman karatun ta mai zurfi.

Ta fara aiki ne a matsayin mai daukar nauyin fim ɗin ta da kanta saboda sha’awar fina-finai don isar da sako ga al’umarta, saƙonni kan canjin zamantakewa. Fim dinta na farko shi ne Tsamiya daga nan sai wani fim mai suna Rabi’a, Rayuwa Bayan Mutuwa, Uzuri da Dakin Amarya.

Hakika Aisha Tsamiya ta nuna wa duniya ita ba kanwar lasa ba ce, domin har yanzu tana ci gaba da bayyanar da hazaka da kwarewarta a fagen finafinan Hausa. Tsamiya ta zama daya daga cikin fitattun ƴan fim goma a cikin jaruman Kannywood a shekarar 2016.

Hakanan Kuma Tsamiya na da masoya da mabiya masu ɗimbin yawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

Fina-finan

  • Tsamiya
  • Ranar Baiko

Hanyar Kano

Bahaushiya

Da Kishiyar Gida

Dakin Amarya

Husna

Jamila

Mai Dalilin Aure (Match Maker)

Makahon Gida

Munubiya

Niqab

Nisan Kiwo

Rayuwa Bayan Mutuwa

Zeenat

Kalan dangi

Aisha Aliyu(tsamiya)

Aisha aliyu tsamiya matashiyar yar film ce data nuna fata da sha’awar shiga masana’antar da shirya fina finan hausa.

An haifi Aisha tsamiya a shekarata 1992 a karamar hukumar nasarawa ta jihar kano, ta tafi makarantar firamare ta Giginyu sannan ta halarci makarantar sakandire.

AikiGyara

Ta fara aiki ne saboda sha’awar da takeyiwa sana’ar shirya fina-finan hausa a cewar ta domin isar da sako ga al’umma. Film din tsamiya shine film din data fara suna a cikin shi, sannan ta fito a film din Rayuwa bayan mutuwa, Uzuri, Dakin amarya, kalan dangi da dai sauran su.

Aisha tsamiya ta zama matsayi na goma a shahararren film din salma, hakika har yanzun Aisha tsamiya tana daga cikin matan da tauraruwar su ta dade tana haskawa a masana’antar shirya film na hausa, kuma ta kware sosai a wannan sana’ar ta shirya fina finan hausa.

ilimiGyara

A halin yanzu dai Aisha tsamiya tana cigaba da neman ilimi a arewa. Aisha tsamiya har yanzun dai batayi aure ba amman tana kiyaye sunanta da duk mutuncinta, sannan tana da burin kammala makaranta kafin tayi aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button