Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Dauda Kahutu Rarara

Dauda Kahutu Rarara wanda aka fi sani da Rarara an haife shine a ( jihar Katsina ) shahararren mawaƙin siyasa ne a Nijeriya, mawaƙi kuma marubucin waƙa,Ni Abdussamad nace Dauda Kahutu Rarara yafi kowa kudi a Kannywood.

Wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen rera waƙoƙin siyasa ga ƴan siyasar All Progressive Congress a babban zaɓen Najeriya na shekarar 2015, musamman ma ga shugaban Najeriya na yanzu Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari.

Siyasar sa

Rarara ya kasance sananne ne yayin babban zaben Najeriya na 2015, lokacin da yake rera wakoki da dama ga Muhammadu Buhari da kuma adawa da shugabancin Goodluck Jonathan a galibin wakokin nasa.

A watan satumba na 2020, Rarara ya nemi gudummawa daga masoyan Muhammadu Buhari, don tura masa Naira dubu daya don sakin bidiyon minti biyu na yabon Muhammadu Buhari, cikin kasa da awanni 48 Ya karbi Naira miliyan 57 don sakin wakar wacce Ya yaba Muhammadu Buhari.

Jerin Wakokinsa.

Dauda kahutu rarara yayi wakoki da dama, ga kaɗan daga cikin fitattun wakokinsa;

  • Masu Gudu-su-Gudu
  • Buhari ya Dawo
  • Baba Buhari dodar
  • Jahata ce
  • Kwana ɗarin Dallatu
  • Kano ta Gandujace
  • Ubban Abba zama daram

Shugaban Kungiyar 13X 13

Shine shugaban kungiyar matasan kannywood ta 13×13, wata kungiya ce ta adadin mutum sha ukku (13), kuma ko wanne mutum daya daga cikin su sha ukkun yana da mutum 13 dake karkashinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button