Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Abdul D One

FIM: Ka na da ra’ayin zama jarumi kamar maigidan ka Umar?

ABDUL: Ina da sha’awar zama jarumi, domin in ka gan ni ma na yi kalan jaruman! Amma yanzu lokaci ne bai yi ba. So, ba a sauri, in Allah Ya so ya kai ka matsayin za ka je. In kuma Allah Ya ga dama ya ce ba za ka yi ba ma gaba ɗaya shi kenan babu yadda ka iya. Amma in Allah Ya nufa na zama jarumin sai ka ga na zama.

FIM: Wace ƙasa harkar waƙa ta kai ka?

ABDUL: Harkar waƙa ta yi mani komai. Amma dai a yanzu fita waje ban a wuce ƙasar Nijar, sai kuma a nan Nijeriya na je wurare da dama sosai. Bayan nan ban je wata ƙasa ba, amma ban a cire rai da zan je in-sha Allahu.

FIM: Ɓangaren nasarori da ka samu fa?

ABDUL: Nasarori ga su nan a zagaye a ofishi na kamar yadda ka ke gani.  Na samu awad da dama. Waɗannan ba ƙananan nasarori ba ne a wuri na. 

Sannan babbar nasara ta a rayuwa, zama da iyaye na lafiya da na ke yi.

FIM: Ƙalubale kuma fa?

ABDUL: Gaskiya ƙalubale ana kan fuskanta a halin yanzu. Duk hanya ta nasara in babu ƙalubale ba a wucewa. Duk abin da ka ke yi in babu ƙalubale a cikin sa ka haƙura da shi kawai, ka canza wani. Saboda mai imani shi ke fuskantar ƙalubale don gwada imanin ka. Duk sana’a ta na da ƙalubale. Allah Ya fitar da mu lafiya.

FIM: Ka faɗa wa masu karatu fitattun waƙoƙin ka da za ka iya bugun ƙirji da su a ko ina.

FIM: Na farko zan iya bugun gaba da ‘Abin Da Ke Rai Na’, ‘Kar Ki Manta Da Ni’; babbar kuma wadda ta danne su ita ce ‘Mahaifiya’, ina bugun gaba da wannan waƙar sosai, sakamakon duk saƙwannin da ke cikin ta abin da ke faruwa yanzu ne.

FIM: Ka taɓa yin kundin waƙoƙi (album)?

ABDUL: Na taɓa yi, amma ba su wuce guda uku ba. Sai wanda mu ka yi da su Umar M. Shariff. A cikin su akwai ‘Na Riƙe So’, ‘Ke ce Tawa’, ‘ Saƙo Daga Zuciya’, sai kuma ‘Tushen Alƙawari’ da zan yi yanzu.

FIM: Ka taɓa yin bidiyo?

ABDUL: Ban yi bidiyo ba, amma zan yi nan ba da jimawa ba.

FIM: A kasuwa ka ke ko kuma akwai ta a ƙasa?

ABDUL: (Dariya) Gaskiya ni ba a kasuwa na ke ba. Ina da wacce zan aura a ƙasa a yanzu haka. Lokaci kawai mu ke jira.

FIM: A ƙarshe, me za ka ce wa masoyan ka?

ABDUL: A kullum ina kira ga masoya na da mu rinƙa haɗuwa da su a shafukan sada zumunci na zamani. Kuma su rinƙa haƙuri da mu, musamman wurin kira. Kuma su ci gaba da saka mu a cikin addu’o’in su. Ina godiya a gare su matuƙa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu