Darajar Naira Ta Faɗi Gabanin Rantsar da Gwamnatin Tinubu
Darajar Naira Ta Faɗi Gabanin Rantsar da Gwamnatin Tinubu
Gabanin kaddamar da gwamnati mai zuwa ta Bola Ahmed Tinubu, Dalar Amurka ta haura zuwa Naira 760, a daidai lokacin da ‘yan siyasa ciki har da ‘yan takarar shugabanin Majalisar Dokokin kasar nan ke yin zagon-kasa wajen neman kudaden kasashen waje.
A ranar 29 ga Mayu, 2023 ne za a yi bikin rantsar da gwamnati mai zsunauwa.
Ana sa ran za a kaddamar da majalisar ta 10 a ranar 13 ga watan Yuni bayan da sabon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu komai ya kama karagar mulkin.
Daily Trust ta ruwaito cewa wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari na biyu zai kare nan da kwanaki 10 masu zuwa.
Wani bangare na masu gudanar da harkokin kasuwar canji ya shaida wa takardar dala farashin ta a dan baya ya karu zuwa Naira 735 a makonni hudu da suka gabata.
Yayin da a wannan karon kuma ta haura zuwa N760 a Abuja a jiya Alhamis.
Daya daga cikin ma’aikatan kasuwar canjin BDC ya ce dala ta samu ribar Naira 12, wanda shi ne mafi girma a ‘yan kwanakin nan.
Dakarun sojin kasar nan sun bayyana cewa basu da kayayyakin da suke da bukata na zamani domin amfani da su wajen gano inda ragowar daliban makarantar sikandiren Chibok suke a yanzu haka, tun bayan da aka yi garkuwa da su a shekarar 2014.
Mai magana da yawun rundunar Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan ne a birnin tarayya Abuja, yayi da yake amsa tambayoyi daga manema labarai yayin wani taro da aka shirya musu.
Ya ce kawo yanzu basu da masaniyar inda ragowar daliban suke, yana mai cewa daliban mutane ne kamar kowa a don haka ne zai yi matukar wuya idan suka ga wasu su iya gane cewa wadannan sune daliban.