E-News
A watan Mayu ne za a fara gasar cin kofin Tarayyar Najeriya – NFF

Hukumar ta NFF ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a karshen taronta na hukumar a daren ranar Litinin a Abuja.
Za a fara gasar mako guda kafin kammala gasar Premier ta Najeriya ta 2022/23.
Wanda ya lashe gasar, da kuma kungiyar da ta zo ta uku a NPFL za ta wakilci Najeriya a gasar cin kofin zakarun nahiyoyi ta CAF a shekarar 2024.
Idan za a iya tunawa dai gasar cin kofin tarayya ta shekarar 2022 ba ta kai ga cimma ruwa ba kuma hukumar NFF ba ta bayyana wanda ya yi nasara ba.
A maimakon haka sai Kwara United ta samu gurbin shiga gasar cin kofin na CAF.