Siyasa

Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Gwamna Rt. Hon. Aminu Bello Masari Ta kashe sama da Biliyan Dari uku Wajen Biyan Albashin Ma’aikatu da Fensho cikin Shekara Bakwai

Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Gwamna Rt. Hon. Aminu Bello Masari Ta kashe sama da Biliyan Dari uku Wajen Biyan Albashin Ma’aikatu da Fensho cikin Shekara Bakwai.

Shugaban ma’aikatan Alhaji Idris Tune ya bayyana haka ne, ranar lahadi 05/02/2023, yayin da yake gabatar da Jawabin maraba, a wajen taron kaddamar da kundin ayyukan Gwamna Aminu Bello Masari cikin waka.

Wanda kungiyar Masari “Modern Singers” tayi. shugaban ma’aikata na Jihar Katsina Alhaji Idris Usman Tune ya ci gaba da yaba ma kungiyar akan kokarinta fadakar da Al’umma akan ayyukan Gwamnatin Aminu Bello Masari.

Shugaban ma’aikatan ya ci gaba da bayyana kokarin Gwamnatin na gudanar da ayyukan raya kasa kama daga bangaren Ilmi, Lafiya, ruwan sha, hanyoyi. Da sauran su, wanda yace” sun lashe kusan biliyan dari, a cikin shekara bakwai da rabi.

Haka zalika ya bayyana kokarin Gwamnatin wajen biyan albashin ma’aikata, fensho, da kudin sallamar ma’aikata idan sun aje aiki watau (Gratuity), da sauran hakkokin ma’aikata. Duk da kalubale da Gwamnatin ta samu kala, kala, Wanda su ka lashe biliyan dari uku da hamsin.

A nashi Jawabin, Babban bako a wurin taron, Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya gode ma kungiyar akan irin goyon baya da gudumuwa da su ka ba shi tun daga zaben 2015, zuwa zaben shekara ta 2019, zuwa yau.

Gwamnan ya bayyana kungiyar a matsayin abokiyar Gwagwarmayar ta siyasa. Daga karshe Gwamnan ya mika kungiyar ga Dan takarar Gwamnan Jihar karkashin Jam’iyyar Apc Dr. Dikko Umar Radda Kungiyar, a matsayin gado.

Tare da jawo hankalin ‘yayan kungiyar da su canja sunan kungiyar daga Masari “Modern Singers”, zuwa Katsina “Modern singers”. Domin dorewar kungiyar, a kada kyamacesu bayan ya tafi.

Shima a nashi Jawabin, babban bako mai kaddamarwa Alhaji Ibrahim Masari ya yaba ma Gwamna Aminu Bello Masari akan dimbin ayyukan raya kasa da ya aiwatar a cikin Jihar Katsina wadanda suke taba rayuwar talaka kai tsaye.

Daga karshe ya kaddamar da kundin ayyukan akan kudi naira miliyan goma, sai ya bayyana Dan takarar mataimakin shugaban kasa na Apc Sanata Kashin Shetima ya kaddamar akan naira miliyan goma.

Sai Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya kaddamar akan naira miliyan biyar, sai Dan takarar Gwamnan Jihar Dr. Dikko Radda naira miliyan uku, sai Sanata Bello Mandiya naira miliyan uku, Dan takarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu naira miliyan ashirin.

Yayin gudanar da taron, Babban malami kuma Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara akan ilmi Mai zurfi Dr. Bashir Usman Ruwan Godiya ya gabatar da kasida akan amfani da mahimman cin fasahar waka a cikin Al’umma, musamman a cikin dimokradiya.

Daga karshe kungiyar ta mika Lambar yabo ga yan majalisar zartarwa ta Jihar Katsina, inda shugaban ma’aikatan ya amshi lambar yabon amadadin yan majalisar zartarwar, haka zalika shima Mai girma Gwamnan, kungiyar ta ba shi lambar yabo.

Shugaban kungiyar Alhaji Ukashatu Ajuba ya mika lambar yabon, tare da taimakon sauran ‘yayan kungiyar, domin nuna farin cikinsu akan Gwamnatin Jihar Katsina, akan yadda ta maida su mutane aka inganta masu sana’arsu ta waka.

Taron ya samu halartar Dan takarar Gwamnan Jihar Katsina na Apc Dr. Dikko Umar Radda, da Dan takarar mataimakinsa Hon. Faruq Lawal Jobe, Sanata mai wakiltar shiyyar Funtua Sanata Bello Mandiya, Engr. Surajo Yazeed Abukur shugaban hukumar gyaran hanyoyi ta Jiha. Dadai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button