Tattaunawa Da Umar M Shareef Akan Rayuwar Sa Da Baku Sani Ba. Akan Soyayyar Wata Nafara Waka.
A INA KA KOYI KARATUN AL’QUR,ANI ?
Ehh to gaskiya tin lokacin da na taso a gidan mu naga a na karatun addini sosai saboda haka nima ba’a barni a baya ba.
IZU NAWA KA HADDACE ?
Ehh, na haddace abin dana haddace amma ba dukkaba.
YA BATUN KARATUN ZAMANI ?
Ehh, karatun zamani ina yi yanzu haka ina KASU A nan Kaduna ina karanta political science.
ME YA JANYO HANKALINKA KA FARA WAKA ?
Sila dalili ne ya kawo in fara Rera Waka Sanadi na soyayya.
Akwai wata baiwar Allah da nagani ina sonta amma na kasa fada mata.
WACE WAKA CE WANNAN ?
Ehh, Amma Fah har yanzu ban Rera Wakar a Studio ba.
TOH YANZU KUNA TARE ?
Aa, Tun wannan lokacin da mukayi haka ban kara neman taba.
KANA BUGA KWALLON KAFA NE ?
Ehh, har yanzu inayin Training saboda kafin nafara waka har kudi a na biyana naje na buga kwallo.
KA TABA JIN CIWO A WAJEN KWALLO ?
Bazai huce shekara daya ba lokacin da na koma Training.
ME KE FARANTA MAKA RAI ?
Abun da ke faranta mini rai shine naje waje a mutuntani.
ME KE BAKAN TA MAKA RAI ?
Idan a ka wulakantani ko a nuna ni ba kowa bane.
DAN RERA MANA WAKAR KA DA KAFI SO ?
Bayan mutuwa ba komai daga kai sai halayyarka.
ME YASA KAYI WAKAR NAN ?
Ehh to abin da yasa nayi wakar saboda na kara tinawa mutane da kaina mutuwa.
AKWAI WAKAR DA KAKE SHIRIN SAKEWA ?
Ehh, gaskiya akwai wakoki masu yawa saboda ina tinanin kundi Zan fitar wanda yake dauke da wakoki 15.
Sai Videos da bansan a dadin suba.
YAYA ALAQARKA DA ABDUL M SHARIFF ?
Abdul dan uwa na ne kuma yayana.
ANA KUSKUREN TANTANCEKU ?
Kwarai da Gaske ana kuskuren hakan kawaii idan mutum yace abdul naga fim dinka zance masa Nagode.
MATANKA NAWA ?
Matata guda daya sunan ta maryam sai yara na guda biyu ALIYU DA HAFSAT.
YAUSHE ZAKA YI TA BIYU ?
Kayi kasa-kasa da muryarka kawaii dai ban shirya bah.
WAI MARYAM YAHAYA BUDURWAR KA CE ?
Aa, maryam yahaya abokiya tace.
WANE ABINCI KAFI SO ?
To gaskiya nafison tuwo miyar kuka ko kuma tuwon shinkafa miyar Taushe.
WANE NE GWANIN KA A CIKIN MAWAKA ?
Ahh, Sadi Sidi Sharifai.
SU WAYE MANYAN ABOKAN KA A MAWAKA ?
Toh, Akwai Lilin Baba, Ado Gwanja, Ali Jita, Nura M Inuwa, Adam A Zango, da sauransu.
Kasance da *Manuniya.com domin samun sabbin labaran kannywood dan samun nishadin Ku . Saboda jin dadinku shine namu.