Yadda Za’a Magance Ciwon Basir Mai Tsiro
Basir mai tsiro ciwo ne dake da wuyan sha’ani sauda dama mutane kansha wahala sosai a kansa wansu kance ma ciwon baya warkewa kuma wannan batu ba haka yakeba, domin babu wata cuta daba maganinta saidai wani lokaci kafin sanin maganin za’asha wahala.
Wannan darasi zai koya maka yadda zaka rabu da wannan cuta ta basir insha Allahu.
Abin Bukata
• Man Tafarnuwa.
• Man Habbatus Sauda.
• Man Zaituna.
• Auduga.
Yadda Za’a Sarrafa Maganin
Zaka hade wannan abubuwa uku wato Man Do afarnuwa, Man Habbatus Sauda, Man Zaitun da muka lissafa baki daya saika gauraye sosai a cikin kwalba kokuma wani abu mai tsafata.
Zaka dauki audigarka daka tanada duk lokacin da zaka kwanta saika dangwali wannan magani daka hada da wannan auduga saika sainya shi a dubararka ma’ana zakayi Matsi dashi.
Zakayi haka har na tsawon sati guda insha Allahu zaku samu lafiya cikin yardar Allah.
Abin Lura:
Yayin yin wannan matsi akwai zafi sai an daure, amma in Allah yarda zaa samu lafiya.