Kunun Aya Na Karawa Namiji Dogon Zango Yayin Saduwa
Matsalan Rashin kuzari da jumawa yayin saduwa, matsalace wanda take damin mazaje da dama wanda hakan na kaiga wasu har rabuwa da abokan zaman su domin basu iya gamsar dasu a yayin tarayyah, Hakan yasa wannan shafi mai Albarka da akoda yaushe yake burin kawo muku abubuwa wadanda zasu taimaka mana ta fannin rayuwa Bangare daban-daban,
Hakan yasa muyi muku binciken wani Abu wanda muna amfani dashi a yau da kullum amma mafi akasari bamusan amfanin sa a garemu ba wannan abu kuwa shine “KUNUN AYA” kunun aya wani abinsha ne da mafi akasarin hausawan mu sun sanshi kuma suna amfani dashi a matsayin abinsha na marmari, shi kuma ana hadashi ne da.
•Aya (Tiger nut)
•Kwakwa (Coconut)
•bushaahen Dabino (Dry dates)
Bayan an tanade su a wanke su, duk wani dattin dake cikin aya da dabino din a tabbata an fiddashi sannan a markadesu a sanya ruwa dan daidai daganan a sanya a freezer yayi sanyi a sha, wannan ba karamin taimakawa yake bangaren mazantaka ba, da sanya mutum yayi dogon zango yana tarawa da abokiyar saduwarsa, fatan Allah ya taimaka.
ku cigaba da kasancewa damu domin samin sabbin shirye shiryen mu Manuniya.com