Ba Sheikh Daurawa ya fadi cewa abinda yafi muni a jikin mace ba shine (farji) Sayyadina Ali (RA) Ne – Prof Mansur Sokoto
Ba Sheikh Daurawa ya fadi cewa abinda yafi muni a jikin mace ba shine (farji) Sayyadina Ali (RA) Ne – Prof Mansur Sokoto.
Bayan karatun shehin malami ashsheikh Aminu Ibrahim Daurawa nacewa babu inda yafi muni da kazanta kamar gaban mace (farji) malam farfesa mansur Ibrahim sokoto ya kawo hujjar da cewa ba aminu Ibrahim daurwa bane kawai yayi fadi sonsa ba a’a ga abinda malamin ya wallafa a shafinsa.
“Ba Sheikh Daurawa ya fadi ba. Sayyidina Ali (RA) ne ya fadi. Ga maganar tasa kamar yadda Sheikh ya fade ta kwabo da kwabo:
قال علي لعمار: “لا تحزن على الدنيا فإنّ الدنيا ستة أشياء : مأكول ومشروب وملبوس ومشموم ومركوب ومنكوح ، فأحسن طعامها العسل وهو بزقة ذبابة ، وأكثر شرابها الماء ويستوي فيه جميع الحيوان ، وأفضل ملبوسها الديباج وهو نسج دودة ، وأفضل مشمومها المسك وهو دم فأرة ، وأفضل المركوب الفرس وعليها تقتل الرجال ، وأما المنكوح فهو النساء وهو مبال في مبال، والله إنّ المرأة لتزين أحسنها فيراد منها أقبحها”. انتهى
تفسير القرطبي – القرطبي – ج ١٧ – الصفحة ٢٥٥
Imamul Qurtubi a cikin tafairinsa (17/255) ya ce: Sayyidina Ali ya ce ma Ammar (RA): “Kada ka samu damuwa akan abin duniya domin jin dadin duniya abu shida ne kawai: Abin ci, da na sha, da na sa wa. Sai kuma abin shaka (turare/kamshi) da abin hawa da na aure.
To, shi dai abincin duniya mafi dadinsa shi ne Zuma wacce fitsarin kuda ce. Mafi kyan abin sha ruwa ne wanda ko dabbobi shi suke sha. Tufafi kuma duk ba su kai darajar alhariri ba; sakar tsutsa ce. Kamshin turare kuma yana a bayan Miski; jinin wata bera ne. Abin hawa mafi daraja shi ne doki wanda a kan sa ake kisan maza. Aure kuma jin dadinsa yana wajen mata; wurin fitsari ne yake haduwa da wurin fitsari irin sa. Wallahi duk adon da ka ga macce ta yi, inda ya fi munin ne ake bukata (Farji)”.
Tafsirin Qurtubi (17/255).
Abin Lura:
Wa’azi akan a kiyayi duniya da kushe jin dadinta sanannen abu ne a cikin Alkur’ani da Hadisan Annabi (S) da maganganun magabatan Musulmi. Su kuma shakiyyan mutane neman wurin kushe Annabawa da karantarwarsu suke yi. Mai imani yana nisantar irin wannan tafarki nasu domin ya tsira da imaninsa.”