HADIZA GABON: Ado Gwanja ya fifita mata akan maza, ya kuma bada zafafan amsoshi ga tambayoyi
HADIZA GABON: Ado Gwanja ya fifita mata akan maza, ya kuma bada zafafan amsoshi ga tambayoyi
Bashin $800m Da Buhari Zai Ciyo Ya Sabawa Kundin Tsarin Mulki — Sanatan Arewa.
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin soji, Mohammed Ndume, ya yi barazanar kalubalantar bashin dala miliyan 800 da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke nema.
MANUNIYA ta tuna cewa Shugaba Buhari ya nemi amincewar Majalisar Dattawa kan rancen dala miliyan 800 daga Bankin Duniya don tallafa wa shirin bunkasa walwalar Al’ummar kasar nan, inda ya bayyana cewa bashin na da nufin tallafa wa talakawa bayan cire tallafin man fetur.
Da yake mayar da martani ga shugaban kasar yayin hirar da ya yi kwanan nan a gidan talabijin na Trust TV, Ndume ya bayhana cewa rancen ya sabawa tsarin mulki kuma ba a yi adalci ba.
Sanatan ya ce: “Zan garzaya kotu saboda bai dace ba, ya sabawa kundin tsarin mulki kuma rashin adalci ne. Bari in ba ka misali, mu biyu ne yanzu a dakin gabatar da shirye-shirye sai ka ce za ka aro miliyan daya ka raba tsakanin mu biyu, yaya za ka zabi biyun, ban da haka, idan ka bayar ga mutum biyun, jdan kuma su ne za su biya, hakan ba laifi bane ; amma wannan fa duk ’yan Najeriya ne za su biya.
“Idan ka baiwa wasu yan Najeriya Naira 4,000 ba tare da kowa ya samu ba, hakan adalci ne? A gaskiya hakan ya sabawa kundin tsarin mulki domin kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba ka damar nuna wariya ba.
“Wadannan mutanen suna amfani da lissafi ne kawai don su rudar da wannan dattijo (Buhari) kuma kawai sai ya amince. Buhari bai fahimci haka ba. Suna son sace kudin ne.
Shugaban jam’iyyar Labour LP, Lamidi Apapa ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi da kuma shugaban jam’iyyar na kasa, Julius Abure da aka dakatar sun dauki nauyin ‘yan daba a kansa (Apapa) a kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, PEPC.
Ku tuna a baya Vanguard ta rahoto cewa wasu fusatattun matasa da ke gaban kotu sun kawo wa Apapa tarnaki domin shaida yadda ake gudanar da shari’ar da Obi ya shigar na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.