Wata Fitsara Da Kwatanta Yin Zinah A Wajen Biki Da Sunan Wayewa Malamai Sun Fusata
Wata Fitsara Da Kwatanta Yin Zinah A Wajen Biki Da Sunan Wayewa Malamai Sun Fusata.
Innalillahi wa’inna ilaihir rajiun watasabuwar masifa data shigo a da ake yi a guraren Biki, wanda aikata abun da yin zina Babu maraba.
Manyan Malam musulun ci sun fusata akan abun saboda Babbar masiface, Mun roƙon Allah ya karemu masu Yi Allah ya shirye su.
Amfani Ruwan Lemon Tsami Agaban Mace
Game da sanadaran da lemon tsami ke kunshe da su, sun hada da Bitamin C da B, sannan da Calcium, irom maganesium, Potasium, Enzimes, antioxidants, da kuma fibers.
Daga cikin sanadaran da mu ka zana a sama, za mu dauki Bitamin C, kadai don bayanin irin fa’idarsa ga jikin dan-adam, hakan zai baka haske kan amfanin lemon tsami ga lafiyarmu. Nazarin zamani ya tabbatar da cewa, shi wannan sanadari na Bitamin C, na iya taimakawa wajem ragewa dan-adam hadarin kamuwa da cututtukan zuciya, da shanyewar barin jiki da hawan jini da sauran su. Idan haka ne wannan dan itaciya na da matukar fa’ida gare mu.
Kar dai mu tsawaita bayani, ga kadan daga cikin amfanin wannan dan-itaciya ga lafiyar dan-adam. A sha karatu lafiya, kuma Allah Ya datar da mu.
1Gusar Da Warin Baki.
Lemon tsami ya shahara wajen gusar da wari. Ban sani ba, ko ka taba jarraba hakan, idan ba ka taba ba, ka gwada, duk lokacin da kaci wani nau’in abunci ma’abocin wari kamar albasa tafarnuwa ko kifi, da zarar ka wanke bakinka da ruwan lemon tsami zai gusar da warin ba tare da wani bata lokaci ba.
Baya ga haka za ka iya amfani da shi wajen tsaftace bakinka ko da ba ka ci wani abu mai wari ba, domin kuwa zai gusar ma ka da duk wani dattin hakori ya sanya bakinka ya yi fes, sannan ya samar ma ka da daddadan numfashi.
Domin samun wannan fa’ida sai a wanke baki da ruwan lemon, hakan zai gusar da dattin hakora. Idan ana son samun numfashi mai dadi sai a sha kofi daya na ruwan lemon bayan kammala cin abinci, ko kuma a sha kofi daya na ruwansa kafin a karya kumullo.
Karanta: Amfanin Tafarnuwa Ga Lafiyarmu.
2. Saurin Narkar Da Abinci.
Ba shakka abincin da mu ke ci kan yi tasiri a jikinmu ne bayan ya narke, kuma rashin narkewarsa kan haifar da kumburi da cushewar ciki. Sanin wannan fa’ida ce ta sanya wasu mutane shan kofi daya na ruwansa domin magance cushewar ciki ko kumburi.
3. Inganta Garkuwar Jikin Dan-adam.
Garkuwar jiki ce ke da alhakin yaki da duk wata cuta da ka iya kawowa jiki hari. Shi kuma lemon tsami na kunshe da sanadarin Bitamin C mai yawa kamar yadda mu ka zayyana a sama. Shi wannan sanadarin ne ke taimakawa wajen inganta garkuwar jikinmu.
Duk lokacin da aka ce, dan-adam ya rasa garkuwa jiki mai kwari, ba wahala duk wata cuta da ta kai ma jikinsa farmaki ta yi galaba a kansa. Misalin da za mu buga don mai karatu ya gane muhimmancin garkuwa a jikin dan-adam, shi ne, kai duba ga cutar da ake kira kanjamau, wata fassarar da ake ma ta ita ce, ‘Cuta mai karya garkuwar jiki’. Abin nufi cutar na ragargaza garkuwar jikin mutum ne don haka ba za ta iya yaki kuma ta samu galaba kan cututtukan da ke kawo hari ga jikinsa ba.
2 Rage Kiba Ko Timbi.
Mutanen dake da girman halitta ko timbi kan fuskanci barazanar kamuwa da wasu cutuka, kamar su hawan jini, ciwon siga da sauran su, kamar yadda bincike ya tabbatar. Baya ga haka, wasu lokutan su kan fuskaci wahalar gudanar da al’amuransu na yau da kullum. Sakamakon haka wasu da yawa ke neman magungunan rage kiba. To ga maganin rage kiba cikin sauki, ga mai son samun wannan fa’ida zai ke shan karamin kofi daya na ruwan lemon tsami, amma zai zuba cikin ruwan dumi ya sha kafin ya ci abincin safe.
5. Maganin Kurajen Fuska.
Duk mai fama da kurajen da ke shafar fuska, musamman kurajen funfus ga matasa mata da maza, za su iya amfani da lemon tsami domin samun waraka daga wannan matsala cikin gaggawa idan Allah Ya amince.
Babban abin farin cikin shine, cikin sauki za a iya magance wannan matsala. Abin yi shine ka samu lemon tsami, ka yanka shi yadda za a samu ruwansa, sai a goga a fuska ko ina, amma a lura saboda ya na da zafi kar ya sami ido. Hakanan yana magance kurajen aska da wasu ke fama da su musamman idan su kai aski. Bayan an yi aski sai a shafe kai da shi, sai dai yana da zafi, a shafa duk lokaci da akai aski, da haka har a rabu da shi.
6. Maganin Rauni.
Sakamakon ayyukanmu na yau da kullum, musamman mata dake mu’amala da wuka lokutan girki, ko kuma su mazan ma’abota aiki da wuka, idan bisa tsautsayi akai wani rauni ko yanka, yin amfani da lemon tsami ka iya warkar da shi cikin gaggawa. Idan haka ta kasance sai a matsa ruwan lemon a kan ciwon, zai kame ya kuma warke da yardar Ubangiji.
7. Taimakawa Ma Su Fama Da Basur.
Ga wadanda ke fama da cutar basur musamman wanda ake kira “Basur mai fitar baya” za su iya samun sauki ta hanya amfani da lemon tsami. Mutanen dake fama da wannan larura ana ba su shawarar gujewa cin abincin da zai haifar mu su da bayan gida mai tauri, saboda hakan ne ke sabbaba mu su tashin basur din. Shan ruwan lemon zai sanya bayan gidansu ya kasance mai laushi, wanda hakan zai haifar mu su da yin bayan gidan cikin sauki.
15. Inganta lafiyar Ido da samar da riga-kafin cutukan da kan shafi ido.
16. Hana yamushewa da yankwanewar fata.
17. Tamakawa hanta fitar da datti daga cikin dan-adam.
: Mu na bada shawara musamman ga ma su fama da larurar gyambon ciki wajen yawaita shan lemon tsami, saboda zai iya haifar mu su da matsala. Idan har su na fama da daya daga cikin matsalolin da mu ka ambata a sama zai fi kyau su nemi wata hanyar maganin tun da akwai wasu hanyoyin da yawa.
Hakanan daga cikin illolin shan sa da yawa, akwai rage sha’awa da kuma haifar da saurin inzali musamman ga maza. Hakanan idan za a shafa a fuska sai a lura sosai kar ya samu ido kuma kar a shafa kuma daga bisani a shiga rana, har sai an wanke. Hakanan mata ma su juna biyu ana ba su shawarar su gujewa yawan shan lemon tsami. Abin nufi anan ya kamata a yi amfani da lemon tsami bisa hikima musamman wajen sha, amma wajen shafawa ba wata matsala kowa na iya amfani da shi.