Biography / Tarihi

Cikakken Tarihin Umar Namadi Dan Modi

Related Articles

WANENE UMAR NAMADI

Alhaji Umar namadi ko kuma dan modi mataimakin gwamnan jahar jigawa Kuma dan takarar gomnan jahar jigawa a jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023.

HAIHUWARSA

Sannan Alhaji Umar namadi wadda wasu sukafi sani da dan modi ko kuma na modi anhaifeshi ne a jahar jigawa a karamar hukumar kafin hausa cikin garin kafin hausa a shekarar alib dubu daya da dari tara da sittin da uku a bakwai ga watan afrilu


Wato 7 April 1963
7/4/1963.

KARATUNSA

Sannan Umar namadi ya faro karatunsane tun daga matakin primary School
Sannan Umar namadi yayi karatunsa na matakin primary School hadi da matakin gaba da primary School wato secondary School duk a cikin garin kafin hausa.


Sannan bayan kammala karatunsa na matakin primary hadi da secondary Umar namadi yawuce izuwa jami’ar

  • (BUK) bayero university kano dake cikin kwaryar jahar kano Inda yayi digirinsa na farko a bangaren
    Accountancy wadda ya gama a shekarar 1987.
    Sannan bayan kammala karatunsa na matakin digiri ya Kara komawa izuwa jami’ar ta garin Kano wato
  • (BUK) bayero university kano inda yayi babbar digiri nashi wato masters a bangaren ilmin harkokin kasuwanci wato masters in business administration (MBA).
    Wadda ya kammala a shekarar 1993.

SHIGARSA SIYASA

Sannan Umar namadi ko kuma dan modi ya baiyana kansa karara a harkar siyasan jahar ne a shekarar 2019.


Lokacin da gwamnan jahar wato badaru abubakar ya daukoshi ya bashi masayin mataimakin gwamnan jahar wanda hakan yana daga cikin abunda yasa ya kara sanuwa sosai a fadin jihar ta jigawa sannan fitowarshi takarar gomnan jahar a zaben shekarar 2023

shima ya Kara bashi damar sanuwa sosai saboda yadda yayi nasarar kada abokanayen hamaiyarsa a zaben fidda goni yayinda ya samu kur’u masu tarin yawa kimanin 1220.


Yayinda mabiyinsa

  • Alhaji sabo nakudu Wanda shima sanata ne mai wakiltar jigawa ta kudu maso yamma a majalisar dattijai a tarayyar nigeria ya samu guda 106.
    Sai kuma shima mabiyinsa wato
  • Ibrahim Hassan sanata mai wakiltar jigawa ta arewa maso gabas a majalisar dattijai a tarayyar nigeria ya samu kuri’u guda 58.
    Sai shima mabiyinsa wato
  • Aminu kani wanda ya kasance dan kasuwane ya samu kuri’u guda 16
    Sai kuma wanda kebinsa a baya a yawan kuri’u wato
  • Faruq aliyu yayinda shikuma ya samu kuri’u guda 13.
    Saikima mabiyinsa wato
  • Sani garin gabas wanda ya kasance shugaban kotun kolin jihar shikuma ya samu kuri’u guda 5.
    Dadai sauransu wadanda ko guda basu samuba .
    Wanda wannan nasarar itace ta bawa Umar namadi damar zama dan takarar gomnan jahar a zaben shekarar 2023 mai gabatowa yayinda dai kara da babban abokin hamaiyarsa daga jam’iyyar PDP Kuma dan sohon gwamnan jahar wato mustapha sule lamido wanda yakasance dane ga sule lamido.
    Dadai sauransu.

AIKINSA

  • sohon kwamishinan kudi. (commissioner of finance)
  • sannan sohon Chairman of Nigerian Association of Small Scale Industries (NASI).
    Sannan Umar namadi ko kuma na modi yayi aiki a ma’aikatu da dama kamarsu
  • yayi aiki a companin dangote bangaren kula da biyan salary.
  • sannan yayi aiki a companin dangote bangaren hulda da jama’a.
  • sannan yakasance ma mallakin namadi umar & co chartered accountant.
  • sannan yarike mukamin shugaban community Bank
  • sannan ya rike mukamin mataimakin gwamnan jahar jigawa sakanin shekarar 2019 zuwa shekarar 2023.
  • sannan shine dan takarar gomnan jahar jigawa a karkashin jam’iyyar APC mai mulkin jahar a zaben da da’a gudanar a shekarar 2023 mai gabatowa.

IYALANSA

Sannan Umar namadi ko kuma dan modi ya kasance yana da mata saidai bincike baigano adadinsu amma damu msiyuwuwa wajen ganin cewa munsamar maku dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu