Siyasa

Ba Za Mu Shiga Zaben Hitar da Gwani Na Gwamna a APC a Taraba da Za a Yi ba.

Ba Za Mu Shiga Zaben Hitar da Gwani Na Gwamna a APC a Taraba da Za a Yi ba.

Yayin da a ranar 10 ga watan Fabrairun 2023, ne za a yi zaɓen fitar da gwani, don zaɓo mutumin da zai yi wa jam’iyyar APC takarar gwamna a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya, da yawan masu neman takarar a jihar sun ce ba za su shiga zaɓen ba.

‘Yan takarar dai sun yi zargin cewa ba a sanar da su game da zaɓen fitar da gwanin ba, sannan an cika Jalingo da sojoji don a razana magoya bayansu.

Matakin da ‘yan takarar suka dauka na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan Kotun Ƙoli ta kori Sanata Emmanuel Bwacha, a matsayin ɗan takarar gwamna.

Injiniya Saleh Mamman, tsohon ministan lantarki na Najeriya, kuma Daya daga cikin masu neman takarar da suka ce sun janye daga zaben, ya shaida wa MANUNIYA cewa, a shafukan sada zumunta suka tsinci labarin za a yi zaben.

Ya ce, “ Ganin a inda muka tsinci labarin zaben, mun fahimci cewa akwai wata manufa daban, gashi kuma ba a sanar damu ba, sannan kuma ko da an yi zaben to ba a yi shi a kan ka’ida ba saboda kotu ta riga ta ce a shari’ar da aka yi ta DSA, babu zabe a jam’iyyar APC a Taraba.

Baya ga wannan shari’a, akwai shari’ar da za ayi ma a ranar 13 ga watan Fabrairun 2023, sannan kuma sai muka ji an ce wai Burutai zai zo zabe, to me zai kawo shi? Gashi kuma ya taho da sojojin da ba ma na kasar ba.” Inji shi.

Injiniya Saleh Mamman, ya ce “ A don haka ba zai yi wu ace za a yi zabe kwana guda ya rage ace ba a gaya mana ba saboda wata manufa da ake da ita, shi ya sa muka cewa to lallai wannan shiri ne, don haka zamu kauracewa zaben.

Dan takarar gwamnan a APC a Taraban, ya ce an ce za a yi zaben fitar da gwanin ne da deliget, to dan takarar mutum daya ne kadai ya bayar da sunayen deliget din da za su yi zaben.

Ya ce, “ Dukkanmu sauran ‘yan takarar mu biyar bamu da sunan mutum daya da muka bayar a matsayin deliget, don haka sai su je su yi abin da zasu yi mu ba zamu je ba don ba zamu karya dokar kotu ba sannan kuma ba zamu je muyi aiki da mutanen da bamu sani ba.

To sai kuma a nasa bangaren, Sanata Emmanuel Bwacha, ya shaida wa MANUNIYA cewa ba wani abu bane ya sa sauran abokan takararsa suka dauki matakin kauracewa zaben fitar da gwanin illa kawai sun tsorata ne.

Ya ce, “ Mu a saninmu rigimar da muke da gwamna ne ba su ba, don haka idan mutum ya kai kara kotu, daga baya kotu ta ce aje ayi zabe, sannan wasu su ce ba za su yi ba me ke nan? Tsoro ne da kuma rashin kyautatawa jam’iyya.

Dan takarar gwamna a jam’iyyar ta APC a Taraba, ya ce dukkansu abokan takarar ta sa bakinsu daya domin sune suka ce a rusa zaben da aka yi a baya don ba su yarda dashi ba.

Ya ce, “ Dama na sha gaya musu cewa ko sau goma za a yi zaben fitar gwani sai na kayar da su.

Sanata Emmanuel Bwacha, ya ce batun cewa shi kadai ne ya bayar da sunayen deliget shi bai san haka ba.

Ya ce, ‘’ Batun zaben deliget fom ake sayarwa kuma suma mutanensu sun saya, don haka basu da wani dalili kawai sun tsorata ne.

Game da zargin da sauran ‘yan takarar suka yi cewa na jibge sojoji a jihar don a razana magoya bayansu, Sanata Emmanuel Bwacha, ya ce rahoto suka samu cewa ‘yan bangar siyasa za su je su hana zaben ne shi yasa aka jibge jami’an tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu