Labarai

An Yi Garkuwa da Wasu Matuƙan Jirgin Sama A Indonesia

An Yi Garkuwa da Wasu Matuƙan Jirgin Sama A Indonesia.

Mayaƙa a yankin Papua na ƙasar Indonesia sun yi garkuwa da wani matuƙin jirgin sama ɗan asalin New Zealand.

An far wa matuƙin, Mr Mehrtens, mai shekara 37 ne bayan da jirginsa mai ɗauke da fasinjoji biyar ya sauka a lardin Nduga mai yawan tsaunuka.

Waɗanda suka sace shi – waɗanda ƴan ƙungiyar TPNPB ne masu ɗauke da makamai – sun shaida wa sashen labaru na MANUNIYA Indonesia cewa yana cikin ƙoshin lafiya.

Amma sun ce ba za su sake shi ba har sai an amince da ƴancin-kai na yankinsu na West Papua.

Mai magana da yawun ƙungiyar rajin ƴancin Yammacin Papua ya ce an saki fasinjoji biyar da ke cikin jirgin kasancewar su ƴan asalin yankin ne.

Hukumomi a Indonesia sun ce za su aika da tawagar masu ceto zuwa yankin, sai dai ƴan sanda sun ce lamarin na da wahala saboda ba a iya isa wurin sai ta jirgin sama.

Firaministan New Zealand, Chris Hipkins ya ce ofishin jakadancin ƙasar a Indonesia na bibiyar lamarin.

Tun farko, ma’aikatar harkokin waje ta New Zealand din ta ce “tana sane” da lamarin.

Ƙaramin jirgin fasinjojin ya tashi ne daga filin jirgi na Mozes Kilangin a tsakiyar yankin Papua a ranar Talata, kuma an tsara cewa zai koma inda ya fito bayan kai fasinjojin.

Dama dai ƴan tawayen na yammacin Papua sun sha yin barazanar kai farmaki kan jiragen sama waɗanda ke ɗauke da kaya ko jami’ai zuwa Jakarta.

Yankin wanda ke da arziƙin ma’adanai ya faɗa cikin rikici ne tun bayan komawa ƙarƙashin Indonesia a 1969, inda yankin ke fafutukar samun ƴancin kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu