Labarai

TIRKASHI: Ƙarancin Naira Da Dan fetur Zai Iya kawo Cikas Ga Zaɓen Nageria Da Bankin Duniya

TIRKASHI: Ƙarancin Naira Da Dan fetur Zai Iya kawo Cikas Ga Zaɓen Nageria Da Bankin Duniya.

Ofishin Bankin Duniya da ke Najeriya ya yi gargaɗin cewa matsalar ƙarancin man fetur da na sabbin takardun kuɗin ƙasar ka iya kawo rashin tabbas game da yiyuwar babban zaɓen ƙasar da ke tafe cikin wannan wata.

Bankin Duniyar ya ce wa’adin da Babban Bankin ƙasar ya saka na daina amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar zai shafi harkokin zamantakewa da kasuwancin al’ummar ƙasar.

Bayanan da bankin Duniyar ya wallafa a shafinsa na internet na cewa “Sakamakon ƙarancin sabbin takardun kuɗi da man fetur wanda aka shafe watanni ana fama da shi a ƙasar. Akwai yiyuwar ‘yan ƙasar su faɗa cikin wahalhalu da matsai, lamarin da zai iya tayar da hankula har ma ya shafi babban zaɓen ƙasar da ke tafe cikin watannin fabrairu da Maris”

Bankin ya ƙara da cewa kashi 45 na matasan ƙasar ne ke da asusun ajiya na banki, kuma kashi 34 cikin ɗari ne ke hada-hadar kuɗi ta internet.

Tun da farko dai Babban Bankin ƙasar ya saka 31 ga watan Janairu a matsayin wa’adin amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar.

To sai dai bayan shan kiraye-kiraye gwamnan Babban Bankin ƙasar ya nemi amincewar shugaban ƙasar domin ƙara wa’adin zuwa 10 ga watan Fabrairu.

To sai dai tun bayan ƙara wa’adin babu abin da ya sauya na ƙarancin kuɗin inda miliyoyin ‘yan ƙasar ke fama da bin dogayen layuka wajen cirar kuɗi kama daga bankuna zuwa na’u’rorin cirar kuɗi na ATM da wajajen masu POS.

Yayin da ‘yan siyasa ke ci gaba da ɗora laifin kan juna, Babban Bankin ƙasar na zargin bankunan ƙasar da ɓoye maƙudan sabbin takardun kuɗin.

Masana dai na ganin cewar bayanan da Bankin Duniyar ya fitar a shafinsa na Internet abu ne da ya kamata a lura da shi, domin kuwa ‘yan ƙasar da dama na ci gaba da fuskantar wahalhalu wajen samun kudin da za su ciyar da iyalansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button