Siyasa

Sanatoci Sun Tattauna Sun Bayyana Wanda Suke Son Ya Shugabanci Majalisar Dattawa

Sanatoci Sun Tattauna Sun Bayyana Wanda Suke Son Ya Shugabanci Majalisar Dattawa.

Dimokuradiyya

Home  Labarai

Sanatoci Sun Tattauna Sun Bayyana Wanda Suke Son Ya Shugabanci Majalisar Dattawa

Zababbun Sanatocin Majalissar ta 10 na yin gangami don nuna adawa da shirin da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ke yi na sanya tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom,………..

Nura Ahmad Hassan by Nura Ahmad Hassan

 April 29, 2023

Reading Time: 2 mins read

18

SHARES

Zababbun Sanatocin Majalissar ta 10 na yin gangami don nuna adawa da shirin da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ke yi na sanya tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom.

Zababbun Sanatoci a zauren majalissar ta 10 na tattaunawa don nuna adawa da shirin da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ke yi na sanya tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa, kamar yadda Daily Trust ta nakalto a ranar Asabar.

An kuma tattaro cewa gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun rabu kan lamarin, inda wasun su suka amince da zabin Asiwaju na Akpabio, yayin da wasu ke ganin ya kamata Arewa ta tsayar da shugaban majalisar dattawa.

Jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito a ranar Juma’a musamman cewa Tinubu ya zabi Akpabio da Jibrin Barau (na jam’iyyar APC a Kano) a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa.

KARANTA HAKANAN Tinubu Na Sasanta Akpabio Da Barau A Matsayin Shugaban Da Mataimaki

Hakan ya biyo bayan ganawa da wasu manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyya mai mulki ciki har da wasu mambobin kwamitin gudanar na kasa (NWC).

Sai dai wata majiya mai tushe ta shaida wa wannan jarida cewa hatta kwamitin NWC na jam’iyyar ya rabu kamar yadda wasu ke son Akpabio, wasu na son Sanata Jibrin Barau daga Kano, yayin da wasu ke son a mika wa yankin Kudu maso Gabas mukamin.

Ku tuna cewa Tinubu ya gana da daukacin gwamnonin APC a ranar Alhamis; kuma a jiya ya gana da gwamnonin jam’iyyar daga yankin Arewa maso Yamma, inda Barau ya fito.

Duk da cewa ofishin Tinubu ya fitar da wata sanarwa bayan taron na ranar Alhamis, inda ya ce an yi hakan ne domin neman goyon bayan gwamnonin wajen gudanar da zaben shugabannin majalisar dokokin kasar ba tare da wata matsala ba, babu wata sanarwa daga taron na ranar Juma’a.

‘Yan majalisa sun yi tawaye

A jiya ne dai alamu suka nuna cewa zababbun ‘yan majalisar musamman wadanda ke komawa majalisar mai jar kujera na adawa da zabar Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawan ta 10.

Hakan dai na faruwa ne duk da tuntubar da Tinubu yake yi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Wasu Sanatoci da aka zanta da su sun ce Akpabio ba zai iya gudanar da harkokin majalisar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu