Labarai

Minista Isah Ali Pantami ya bawa jarumi Nuhu Abdullahi babban mukami a hukumar NIMC

Ministan sadarwa Isah Ali Pantami ya bawa jarumi Nuhu Abdullahi babban mukami a hukumar NIMC.

Ministan sadarwa “Farfesa Aliyu Isa Pantami” ya gwangwaje jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi da babban mukami a ma’aikatarsa, kamar yadda shafin “labran hausa” suka ruwaito.

Kamar yadda su ka wallafa wata takarda mai dauke da tambarin masana’antar sadarwa, an nuna yadda Ministan ya bai wa jarumin mukamin jakadan ranar NIMC da za’a yi ta shekarar 2022/2023.

Kamar yadda takardar ta nuna, dalilin ranar shi ne wayar da kan jama’a dangane da hakkinsu, ayyuka da damar su a tattalin arzikin kasa.Kuma hakan dama ce wacce zata nuna ayyukan gwamnati karara dangane da NIMC.

Mukamin na shekara daya ne cur kuma zai fara aiki ne a ranar I6 ga watan Satumban 2022 zuwa ranar 15 gawatan Satumban 2023, za’a iya sabunta nadin sa amma sai an ga yanayin kwazonsa a aikin.

Har ila yau, ma’aikatar NIMC zata iya lokaci bayan lokaci gayyatarsa don wayar da kansa dangane da harkar lambar katin dan kasa da kuma harkoki masu kama da hakan da sauransu.

Muna taya jarumin murna da fatan Allah ya taya shi riko. Ameen Ameen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button