Labarai

‘yan sandan jihar Kano sun gurfanar da ɗan China a gaban kotun bisa zargin kashe tsohuwar budurwar sa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da ɗan kasar China Mista Geng a gaban babbar kotun majistare da ke zamanta a Normansland a jihar Kano bisa zargin kashe tsohuwar budurwar sa Ummulkulsum Buhari.

Rundunar ‘yan sandan ta tuhumi mai laifin ne da laifin kisan gilla da aka yi wa matashiya ‘yar shekaru 23 da ta kammala digiri a jami’ar Kampala da ke Uganda, a cewar kakakin ‘yan sandan.

Idan za a iya tunawa, an zargi wani dan kasar China mai suna Mista Geng da ya kashe tsohuwar budurwarsa, Ummukulsum Buhari a gidan su a kuntau unguwar Janbullo a jihar Kano.

Wannan mummunan lamari ya faru ne da karfe 7 na yammacin ranar Juma’a, inda aka ce Geng ya samu hanyarsa ta zuwa gidan marigayiya Ummukulsum.

An ce Ummukulsum Buhari ta kammala karatun digirin digirgir a fannin aikin gona a jami’ar Kampala ta kasar Uganda, kuma bayan kammala karatun ta tana yin hidimar bautar kasa (NYSC) a Sokoto.

Wata majiya ta shaida wa Jaridar Manuniya cewa Mista Geng ya yi soyayya da budurwar tsawon shekaru biyu kafin ta yi Aureda wani mutum a Kano.

Sai dai auren Ummukulsum Buhari bai jimaba suka rabu da wanda ta aura, daga nan ta koma gidan su ta cigaba da rayuwarta ta yau da kullum.

Labarin ya bayyana cewa Mista Geng, wanda ya ji haushin zargin da Ummukulsum Buhari ta yi na ƙin auren sa, ya kutsa cikin ɗakinta ya yanka ta a maƙogaro jinni ya ringa zuba.

Wani rahoto ya ce wasu da suka yi kokarin ceton rayuwarta sun kai ta asibitin da ke kusa, inda ajali yayi halinsa ta rigamu gidan gaskiya.

Jami’an ‘yan sanda sun kubutar da wanda ake zargin daga hannun ‘yan ta’adda inda aka kai su ofishinsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button