Labarai

Tattaunawar Malam Daurawa da Ummita a satin da Dan China ya kashe ta

Tattaunawar Malam Daurawa da Ummita a satin da Dan China zai kashe ta.

KARANTA: Tattaunawa Tsakanin Malam Aminu Ibrahim Daurawa da margayiya Ummita (Wadda Saurayinta dan China ya kashe a Kano)

*A satin da Dan China zai kasheta ta kira Malam Daurawa .

  • SunySunyi minti 15 tana tambayar Malam shawara akan ko zata iya Auren Dan China din.
  • Ta tabbatarwa da Malam cewa Dan China ya musulunta.
  • Ta fadawa Malam cewa iyayenta sun hana Auren basa son shi da ita.
  • Tace yana sana’ar hakar ma’adinai a Bauchi.
  • Sun gama waya akan cewa zata yi wasu abubuwa 5 da Malam Daurawa ya shawarce ta daga nan shi kuma Malam zai shigo lamarin zai sami iyayen nata domin a barsu suyi aure.

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana kaduwarsa game da rasuwar Ummukulsum (Ummita) wacce ake Zargin Saurayinta Dan China ya kashe inda Malamin ya ce ko sati ba ayi ba sai da ta kira shi a waya tana tambayarsa shawarwari akai.

Manuniya ta ruwaito margayiyar ta shaidawa Malam Daurawa cewa tana son ta Auri Dan China amma iyayen ta sun ki duk da cewa ya musulunta kuma yana aikin hakar ma’adinai ne a Bauchi,

Malam Daurawa yace a lokacin ya bata shawarwari guda Biyar kuma ya gaya mata da zaran ta aiwatar dasu ya dauki alkawarin shi zai ja gaba ya samu iyayenta ya lallaba su ayi Auren,

Kwatsam ko sati ba ayi ba sai dan China yayi gajen hakuri inda ya aiwatar da wannan danyen aika-aika ya kasheta, inda Malam yayi kira da a bi mata hakkintaGa yadda tattaunawar Malam Daurawa da margayiya Ummita ta kaya….

Malam Daurawa ya ce “Sati guda da ya wuce (Ummita) ta kirani a waya tace malam ina da tamabaya ina ta neman wayarka ban samu ba, Inaso zan auri wani dan China amma iyaye na sun ki yarda,Nace to iyayenki sun fadi gaskiya kada ki auri wanda baki san asalinsa daga inda ya fito ba, don haka zan baki shawara guda Biyar,”

Manuniya ta ruwaito Malam Daurawa ya ce “Shawara ta farko a nemi Immigration su tabbatar da cewa (Dan China din wato Mista Geng) yana zaune a Najeriya da iziniSannan na Biyu, me yake yi a NajeriyaSannan na Uku nasan Sarki a baya ya nada Sarkin yan China mazauna Kano to a sanar dasu suyi bincike akansa sun san shi sun san garinsu sun san daga inda ya fito sun san me yake yi?”“Sannan na hudu akwai ofishin jakadancinsu ma,

ya kamata su ma a sanar da su cewa wani dan China yana so zai auri wata yar Najeriya kaga sai ya zama na farko ofishin jakadancinsu ya sani, Immigration da suke kula da shige da ficen baki sun sani, sannan sarkin yan china da suke zaune a Kano ya sani, sannan kuma nace a hadaku da Hisbah, tunda tace ya musulunta nace to aje a fara koya masa addinin musulunci tukunna har ya iya addinin musulunci”

Manuniya ta ruwaito Malam ya cigaba da fadin cewa “Nace saboda kada ayi auren daga baya ya gudu ya barki da ya’ya ko kuma aje garinsu…

tace ai anyi waya da yan uwansa sun ce sun yarda yan’uwana ne suka ce basu yarda ba nace to ai gaskiya suka fada,”

“Amma idan akayi wadannan matakan guda Biyar to ni zanyi magana da yanuwan naki sai inyi masu bayanin cewa su gamsu, amma in daya daga cikin abu biyar din nan aka rasa shi, na farko bai da takardar zama (to da matsala),

nace a ina yake sana’a ta ce ko suna hakar ma’adinai ne ko a Bauchi ne ko a ina ne, haka dai muka tattauna wajen tsawon minti 15 da ita (Margayiya Ummita).Manuniya ta ruwaito Sheikh Daurawa ya rarrashi Ummita da cewa

“Nace hakuri zakiyi abi matakan da iyayenki suka fada har a tabbatar da wadannan abubuwan guda Biyar, kinga idan anyi Aure musulunci bai hana dan wata kabila da wata kabila (suyi aure) ba, (musulunci) ya ma hana kabilancin to amma dole ayi aure da wanda ansan wa aka aura,”

“Har na bata misali da wata a Kaduna wacce mijin ta ya gudu ya barta da ya’ya kusan Biyar ba asanshi ba ba asan komi game dashi ba..

nace to kinga wannan abu da ya faru da waccen mata to kada ke ma ya faru gareki, tace to ta gode ta gode za ayi (wadannan abubuwan Biyar da na lissafa mata).”Sai dai Manuniya ta ruwaito Malam ya tambaye ta ko dan China Musulmi ne

“Nace ya musulunta (ne) tace eh ya musulunta nace to Alhamdulillah sai a koya masa musulunci…”“Bai fi sati guda ba… to sai kuma naji ance wani dan China ya kashe wata (sai) naji takaici kwarai da gaske wannan abun bakin ciki ne abun takaici ne”

Manuniya ta ruwaito Malam ya rufe da addu’ar “Allah ya jikanta Allah ya yafe mata shi kuma Allah yasa a dauki matakin da ya dace a kansa domin kada haka ya cigaba da faruwa (anan gaba).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button