Labarai

Daka Gina Masallaci Ko Islamiyya Gwara Ka Bawa Yan Fim Kudin Suyi Shiri Me Fadakarwa – Inji Momo

Daka Gina Masallaci Ko Islamiyya Gwara Ka Bawa Yan Fim Kudin Suyi Shiri Me Fadakarwa – Inji Aminu Sharif Momo

A cikin binciken da muka sabayi don kawowa mabiya wannan shafi labarai da rahotanni, yau munyi karo da wani ala’amari me daure kai wanda ya sa mutane suke ta maida martani.

Lokacin da akai hira da Jarumi Aminu Sharif Momo da aka tabo maganr bada Zakkah yayi magana kan cewa tabbas suma yan fim suna buqatar tallafin zakka domin su fina finai masu fadakarwa.

Kamar yadda zamu shaida muku, MANUNIYA.COM ta samo wannan rahoto ne cikin wani shashin hira da gidan rediyon Freedom Kano sukayi dashi jarumin wannan suku wallafa a shafinsu na Facebook.

Cikin hirar dai Aminu Sharif Momo yayi kira ga a dinga bawa yan wasan kwaikwayo Zakkah inda yake cewa da mutum yaje yana gina Masallatai ko Islamiyyu gwara ya bawa yan fim kudin don su shirya fina finai masu fadakarwa.

Saboda haka a cikin wannan sautin murya zaku yadda dan wasan kwaikwayo ya jadda maganar na cewa yana da kyau a kama fitar da kudi ana shirya fina finai maimakon a kama gida masallatai da islamiyoyi.

Zaku Iya sauraron abun da Jarumin yace a nan ƙasa. 👇👇

Wannan magana da yayi hakika ta fusata mutane wanda suketa ajiye martani na nuna rashin jin dadinsu akan wannan furuci nasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button