Labarai

Ana yiwa Rayuwa ta barazanar kisa saboda nace dole sai ayi rajistar SIM -inji Pantami

Daga Manuniya

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na kasa, Farfesa Isa Pantami, ya ce rayuwarsa na fuskantar barazana saboda tsarin da ka kirkiro na rajistar layin waya da haɗa Lambobin dan kasa na NIN da SIM.

Ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata yayin da yake jawabi a wajen taron ranar hada NIN da SIM da aka gudanar a Abuja, babban birnin tarayya.

HOTON :- Ministan Sadarwa

Manuniya ta ruwaito Pantami wanda ya bayyana wasu fa’idodin NIN din ya ce mutane da yawa masu mugun nufi sun tashi tsaye akansa suna sukar sa game da neman kawar dashi.

Baya ga barazanar da ake yi wa rayuwarsa, Taskar Labarai ta ruwaito ministan ya kuma yi zargin cewa wasu su dukufa daukar nauyin batanci kan wannan tsari na NIN duk don saboda a dakatar da shirin.

An shirya taron ne domin tunawa da ranar yin NIN karo na hudu kuma taken taron na bana shine ‘Sarakunan Gargajiya a matsayin masu ruwa da tsaki a harkar wayar da kan jama’a”

Manuniya ta ruwaito Shiekh Isa Ali Ibrahim Pantami ya sha nanata cewa ya shigo da tsarin yin rajistar NIN a wayoyin salula ne domin a inganta tsaro a Najeriya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button