Labarai

Gaskiyar abun da ya faru tsakanin Ummi da ɗan kasar China ɗin daya kasheta

Gaskiyar abun da ya faru tsakanin Ummi da ɗan kasar China ɗin daya kasheta jiya a Kano.

Wani dan kasar China ya kashe wata budurwa a Kano.

Wani Dan kasar China Geng Quanrong ya kashe wata budurwa Mai suna Ummukulsum Sani ta hanyar caccaka mata wuka.

Hoton Ummukulsum da ɗan China daya kasheta

Acewar Rundunar ‘Yan sandan jihar Kano Lamarin ya faru ne a unguwar Dorayi Babba da ke nan Kano.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaidawa Premier Radio cewa Dan Chinan Mai shekaru 47 ya haura har gidan su yarinyar ne ya kashe ta.

Dan Chinan dai na zargin Ummukulsum da yaudararsa, ta hanyar kin aurensa bayan ya Dade yana yi mata hidima.

Wannan shine hoton Ɗan Chinan da Ummukulsum

Hakan ce ta sanya ransa ya baci ya kuma je har gidansu dake unguwar Yamadawa a Dorayi Babba ya haura cikin gidan don aiwatar da mummunar manufarsa.

Bayan ya haura ne ya shiga dakin yarinyar ta taga, ya zaro wuka ya fara caccaka mata a wuya da kafadunta.

A cewar Kiyawa bayan samun Labarin ne kwamishinan yan sandan Kano ya tura jami’ansa karkashin DPOn Dorayi Babba CP Abubakar Lawan.

Ya ce da isarsu ne suka dauki yarinyar zuwa Asibitin Murtala inda likita ya tabbatar da da mutu.

Kiyawa ya ce tuni Suka damke wanda ake zargi kuma an mayar da shi shalkwatar Yan sandan domin ci gaba da bincike.

Ga bidiyon yanda samarin unguwar suka so su kashe ɗan Chinan, Amma Allah ya kawo ‘yan sanda suka ƙace Shi.

GA BIDIYON 👇👇

Allah sarki! Ummukulsum kamar ta san ta kusa mutuwa tayi wani tayi wani Video ita da ƙawar ta Khadija, bayan mutuwar murgayiyar aka fito da Bidiyon.

Zaku iya Kallon Bidiyon anan kasa 👇

Ga Cikakken bidiyon Bayani Anan kasa zamu kawo muku don ku saurara

GA CIKAKKEN BIDIYON 👇👇

Ku kasance da MANUNIYA.COM don cigaba da samun sababbin labarai da Ɗumi Ɗumin sa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button