Kannywood

Ana Cece Kuce Akan Mutuwar Auren Ado Gwanja Da Matarsa Maimuna

Ashe Wannan Dalilin Ne Yasa Ado Gwanja Yasaki Matar Sa Maimuna.

Kamin Ki Bashi Damar Ya Turo Gidanku Ki Tabbatar Da Wadannan Abubuwan Guda 5:

#Tsangayarmalamtonga

SHARE

Duk da ana samun wasu iyayen suke zabawa ‘ya’yansu mata mazan da zasu aura, sai dai mafiya yawan iyaye suke baiwa ‘ya’yan nasu damar zaban wanda suke so su aura da kansu. Wannan kuma shi abunda musulunci ya aminta da shi saboda gudun kada ayiwa yarinya auren da bata so.

Sai dai kuma duk da irin daman da iyayen suke baiwa ‘ya’yan nasu na zabin wanda suke so da kansu, iyaye basu damu su daura yaran nasu akan wani ma’aunin da zasu tabbatar da mijin daya dace dasu ba kamin su gabatar da shi ko bashi damar turo iyayensa. Mafiya yawan iyaye muddin ‘yarsu tace ta samu wanda zata aura abunda suka fi damuwa da su sani shine idan tana son shi da gaske. Wanda tabbatar da hakan shikenan a wajen su ta samu miji tunda dai itace tace tana sonsa.

Wannan matakine ko sakacine da iyayen da suka maida soyayya zalla ya zama shine abun auna mijin da ‘yarsu zata aura.

Da yake ita kuma wacce ake son babu wani tsani da aka daurata akai na alamun mijin da zata aura, duk wanda ya zo mata da iya magana, kwalliya ko kudi shi kenan a wajenta ta samu mijin aure.

Kada ki baiwa namiji soyayyar ki. Kada ki bashi damar ya aureki. Kada kicewa namiji ya turo gidanku har sai kin tabbatar da wadannan abubuwan kamar haka:

#SHAWARA

1: Dagaske Yana Sonki: Maza dayawa ba abun kunya bane su furta miki kalmar soyayya, amma ba hakan suke nufi ba. Akasarin maza mayaudara da sha’awa ce ke kawosu wajen mace da kalmar soyayya suke zuwa.

Shi kuma soyayya bada fatar baki ake furta shi ba a aikace ake nunawa mutum har sai na kusa dashi bama shi da ake son ba sun tabbatar da ana maki soyaya na gaskiya.

A darusan mu na baya mun kawo hanyoyin da mace zata fahimci na miji dagaske yake sonta da dama. Don haka ba sai mun sake nanatawa ba.

Sai dai cikin abubuwan da zaki iya fahimtar namiji yana sonki dagaske sun hada da:

Zai damu dake da kuma bukatunki. A duk lokaci yana son ji duriyarki da halin da kike ciki. Yana shiga tashin hankali a duk lokacin da yaji wani abun maradadi ko mara kyau ya samenki. Duk inda yaga wani na kusa dake yana mutuntasu.

Da zaran kin fahimci wadannan abubuwan daga mai sonki da aure akwai alamun dagaske yake sonki. Sai dai soyayyar da yake miki kadai basu isa kice ya turo ba.

Haka wasu da Sana’o’in nasu bai kai ya kawo ba amma sai manyan hidima suke yiwa wacce zasu aura, su kuma saboda kwadayi sai su fada soyayya ba tare da la’akari da abunda zai je ya zo ba.

#Shawarace

Hadari ne babba ki amincewa namiji yaga iyayenki baki tabbatar da aiki ko sana’ar da aka sanshi da su ba.

4: Addini Da Akida: Akwai mutane da dama da a zahiri ana musu kallon Musulmai ne kuma ana mu’amala dasu a matsayin musulmai amma sam ba musulmai bane.

wadannan abubuwan idan sun tashi aure suke jefasu a kullum suke danasani kuma suke kukan maza sun yaudaresu.

Abun haushi akasarin mata sun gwammace suyi aure kona mako guda ne su fito maimakon su hakura suyi auren daya dace. Mafiya yawan mata ba matakan zaman auren suke dubawa kawai kwanciyar auren shine abunda suke zumudinsa.

Abunda yasa ki tabbatar da wadannan abubuwan da kanki kamin ki amincewa mai sonki shine, ba kowa zai tsaya ya miki wadannan abubuwan ba sai idan kinyi sa’a iyaye ko magabata masu kula.

Wasu iyayen ko magabatan daman kin ishesu kawai su suke kiyi aure duk abunda zai faru kawai ya faru.

Ki sani, illar kiyi aure ki fito yafi illar zama ba auren sauki. Don haka idan ke baki tausayawa kankiba ba kowa ne zai tausaya miki ba, har na tare dake..

Da fatan zaku daure kuyi amfani da wadannan shawaran domin amfanin kanku.

‘Yan Mata Ga Wasu Kalaman Zuga Saurayinki Idan Ya Tambayeki Me Yasa Kike Sonsa:

SHARE 

#Tsangayarmalamtonga

Maza da yawa sukan nemi sanin dalilin da mace take sonsu. Da haka ne wasu mazan suke fahimtar gaskiyar Soyayyar da mace ke musu.

Ga wasu kalaman da zaki zuzuta duk wani mai sonki da aure daya tambayeki dalilinki na sonsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu