Labarai

Wata Mata Ta Haifi ‘Yan 4 Bayan Ta Kwashe Shekara 7 Bata Haihuwa

YANZU – YANZU :- Wata Mata Ta Haifi ‘Ya ‘ya Huɗu Bayan Ta Kwashe Shekara 7 Bata Haihuwa, Ikon Allah.

DAGA MANUNIYA

Wata kyakykyawar mata ta haifi jarirai guda hudu masu ban sha’awa bayan ta kwashe shekara bakwai ba ta daɓa haihuwa ba.

A Wani faifan bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta a jiya ya dauki hankalin Mutane, inda ma’aikatan lafiya masu karɓar haihuwa suka fito da jariran daga dakin haihuwa An yi Kyawawan jariran ado da kwaliya a cikin wani faifan bidiyo mai sosa rai da ban sha’awa.

Bidiyon mutane da dama sun gansa a shafukan sada zumunta. Yayin da wasu mata ke fatan haihuwar tagwaye, wasu kuma sun cika da kyan jariran hudu.

“Duk mai haƙuri yana take da nasara a Rayuwar sa, Uwar jariran ta ta yi addu’a ga tagwaye amma Allah ya albarkace ta da ‘yan hudu. Tai ta murna, “Bcrwordlwide ya rubuta.

Zaku iya Kallon Cikakken bidiyon a nan ƙasa. 👇👇👇👇👇👇

DAG MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button