Labarai

Ambaliyar Ruwa Tayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 13 a Plateau

DA ƊUMI – ƊUMI :- Ambaliyar Ruwa Tayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 13 a Plateau da Gidaje 220 da Amfanin gona da Dama.

DAGA MANUNIYA

A ranar Litinin da daddare ne al’ummar karkara 13 a karamar hukumar Langtang ta Kudu da ke jihar Filato suka fuskan ci ambaliyar ruwa da ta lalata dukiyoyin jama’a.

Jarida Manuniya rawaito cewa ambaliyar da ta afku tayi sana diyar mutuwar mutun 13, inda ta rutsa da gidaje kusan 220 tare da amfanin gona da dama.

Mazauna yankunan da lamarin ya shafa sun shaida wa wakilin jaridar LEADERSHIP cewa ruwan sama mai karfi da ya dauki tsawon sa’o’i da dama a daren ranar Litinin ya kai ga lalata kadarori.

Wani mazaunin Mabudi Emmanuel Nanpak ya ce gidaje da dama sun nutse a cikin Mabudi Lashel,Turaki,Gehetu,Karkasi Magama da sauran al’ummomi.

Nanpak, wanda ya yi ikirarin cewa ya yi asarar duk abin da ya tanadi rayuwarsa, ya nemi taimakon gwamnati.

Wani mazaunin garin wanda ya bayyana sunansa Nankar Adams ya ce bala’in ambaliya na nuni da “yunwar da ke tafe a yankin,” saboda manyan manoma da dama sun shafa.

A halin da ake ciki, shugaban karamar hukumar Langtang ta Kudu Vincent Venman Bulus a shafinsa na Facebook ya ce “abin bakin ciki ne da jin labarin Ambaliyar ruwa da ta mamaye al’ummar Mabudi na Langtang ta Kudu wanda ya yi sanadin lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.

“Ina jajantawa wadanda ambaliyar ta shafa da kuma daukacin al’ummar Mabudi.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button