Labarai

Wasu Kura kuren Da Sabbin Ma’aurata Ke Tafkawa

Wasu Kurakuren Da Sabbin Ma’aurata Ke Tafkawa.

Wasu daga cikin abubuwan da suke jawowa ma’uarata matsala sune irin kuskuren da suke yi tun suna sabbin ma’aurata. Wanda suka kasa fahimtar kuskure ne ko kuma sun sani sun bi son ransu.

Zaman aure tamkar yiwa yaro tarbiya ne. Da irin tarbiyan da ka masa da shi zai taso. To haka Zamantakewa rayuwar aure yake. Yadda kuka soma shi tun kuna sabbin ma’aurata da wannan zamanku zai dore, ana samun akasin hakan bayan kun saba da shi ana iya samun matsala.

Ga wasu kurakuren da akasarin sabbin ma’aurata suke yi wadanda kuma suke zame masu matsala daga bisani.

1: Sabawa Juna Da Abunda Ba Zai Dore Ba: Muddin ma’aurata suka biyewa dokin amarci suka shigo da wani dabi’a ko halin da suka san bazai dore ba to a gaba ana iya samun matsala.

Misali namiji ya ce duk abunda matarsa ke so zai mata shi a kuma lokacin data ke so. Muddin ya saba mata da hakan duk randa ya kasa yin hakan zai iya fiskantar matsala daga gareta. Ko kuma yace a kullum sai ya shigo mata da wani abinci ko abun sha datake so. Ba kowace mace bace take iya yin uzuri da wannan sabon a lokacinda taga an kwana biyu ba a mata hakan ba.

Wasu aiyukan gida na kyautatawa da ba lalle bane mace tayi su, irin debo ruwa a famfo ko rijiya, zuwa kasuwa cefene, yiwa miji wanki ko guga, muddin tasan bazat dore da aikata irin wadannan aiyukan ba kada ta sabawa miji da yinsu. Saboda duk randa aka kwana biyu bata yi su ba zai iya zamo musu matsala.

2: Rashin yiwa juna gyara: Idan ma’aurata suka saba da duk abunda kowa yayi dai-dai ne, to daga randa wani yayi kokarin gyara wa guda kuskurensa za a iya samun matsala.

Dole ku sabawa baiwa junanku shawarar da kuma yiwa juna gyara a wani kuskure tun kuna sabbin ma’aurata. Hakan zai sa gaba wani ba zai ga abun a matsayin raini ko kiyayya yasa da ba ayi amma yanzu an tsiro yi.

3: Ci Gaba Da Soyewa Irin Na Kamin Aure

Soyayya kamin aure da kuma soyayya bayan aure suna da bambamci. Soyayya kamin aure masoya na iya fita yawon shakatawa duk inda suke son shiga. Soyayya bayan aure dole ma’aurata suyi la’akari da wurin da zasu shiga. Masoya suna iya fita yawon a duk lokacin da suka tsara. Soyayya bayan aure hakan zai iya samuwa ne kadai a lokacin zuwa lokaci saboda matsaloli na rayuwar aure.

A soyayya kamin aure duk wasu bukatu na masoya sukan yi kokarin biyawa juna. Soyayya bayan aure bukatun da suka zama dole kuma masu mahimmanci su ake kulawa. Duk zuwa wajen mace a lokacin soyayya kamin aure sai saurayi ya je mata da wani abun kwalama ko kuma ya mata kyauta musamman ga mazan da ba kullum suke zuwa ba. Amma shi soyayya bayan aure wani lokacin ma miji zai dau lokaci ba tare da yana da abun zai kawo gidan nasa na dole bare kuma na kyauta.

Ire iren wadannan abubuwan dole ne sabbin ma’aurata su saka a ransu ba irin soyayar da suka yi kamin aure ba zasu yi bayan aure ba. Hakan kuma ba yana nufin basa son junan su bane sai dai yanzu Zama ne na har abada dole ne su rika yin abunda zasu iya ci gaba da yin sa.

4: Samun ‘Yanci: Daga lokacin da sabbin ma’aurata suka baiwa kansu ‘yancin yin abunda suke so a lokacin da suke so, gaba zai iya zamemasu matsala idan suka yi kokarin neman gyarawa.

Kada ango yace zai bar matarsa tayi abunda take so, ta je inda take so a lokacinda take so. Ko tayi shiga irin yadda taga dama. Idan ya kauda kai a yanzu saboda soyayya to gaba zai iya yin wuya yace zai gyara lamarin ba a samu matsala ba.

Haka itama mace kada ta kauda kai ta bar mijinta yana yin abunda bai kan ka’ida saboda tunanin yanzu suka yi aure.

Fita hiran banza majalisa tun kuna sabbin ma’aurata zaki nuna masa baki so. Dawowa gida lokacinda mijinki yaga dama ba tare da hujja abun kamawa ba yanzu zaki takawa hakan burki. Hira da wasu matan a waya a gabanki kada ki bari ya saba tun yanzu. Cin fuska ko zagi tun kuna sabbin ma’aurata zaki hanashi idan kin fahimci yana neman shigo da su.

5: Jima’i: Idan ma’auratan nan yanzu suka taba aure, to kada su sabawa kawunansu yin Jima’i da nan gaba zai iya cutar da su. Kada ya zama sabon ku da Jima’i a lokacin amarci zai iya takura guda daga cikinku idan hakan bai samu ba a lokacin da ake bukata. Don haka ku sabawa juna abunda zaku iya ko da nan gaba an samu lalura na rashin lafiya ko kuma tafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button