Labarai

Tofa An Kama Wani Mutum Bisa Yiwa Yar Cikinsa Fyaɗe Yau

Tofa an kama wani mutum Bisa Yiwa Yar Cikinsa Fyaɗe.

Wani magidanci ya zabi ya dinga kwanciya da yarsa duk da cewa shi ya haife ta kamar yadda muka samu labari.

Rahoton da amihad.com ta samu ya tabbatar mata da cewa: wata ýar kasuwa dake zaune a Ibadan, Misis Aminat Adeshina a ranar Litinin, 15 ga watan Ogusta ta bukaci wata kotun Ile-Tuntun, Ibadan da ta raba auren ta da mijinta Akeem Adesina na tsawon shakara 22 kan zargin neman lalata da ýar su.

A korafin ta, Amina wacce ked a ýaýa hudu t ace mijin nata ya yi yunkuin yiwa ýar su mai shekaru 16 fyade.

A cewar ta bayan ta bar gidan shi saboda rashin kula sai ya koma yunkurin lalata ýar su da ta bari a wajensa.

Da farko ýar tasu ta fada mata cewar wani ya shigo dakinta yana yi mata lalube a jiki, don haka sai washe gari ta fara tsine ma mutumin da basu san ko wanene ba a gaban mahaifin ta.

Amina ta ce ýar ta su ta fada mata cewa mahaifinta yayi kokarin siye ta da naira 1000.

Sai dai wanda ake karan bai ce komai ba akan zargin da ake masa. Yace matarsa ta yasar das hi lokacin da yake da tsananin bukatar ta.

Kan zargin kokarin yiwa ýar su fyade Adesina ya ki cewa komai.

Cif Henry Agbaje, alkalin kotun ya dage sauraron shari’an zuwa ranar 22 ga watan Ogusta inda ya bukaci da su kawo hujja domin marawa zarginsu baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button