Labarai

Wasu Nauikan Mata Guda 5 Da Basu Cika Zaman Aure Ba

Wasu Nauikan Mata Guda 5 Da Basu Cika Zaman Aure Ba.

A lokacin da wasu matan burinsu suyi aure sai mutuwa zai rabosu da gidan mazansu. A hakan kuma akwai matan da basu ma damu da auren ba, wasu kuwa idan ma sunyi aure basu ciki zama a gidan auren nasu ba. Ga irin matan nan guda 5 domin kaucewa maza asaran kudi da lokaci.

  1. Mata Kyawawa:

Su mata Kyawawa a kullum cikin yaudaran kansu suke yi da wannan kyau da Allah Ya musu.

Ganin yadda maza suke musu chaaaaa, na bukatar aurensu, hakan yasa koda sunyi aure abu kadan zai hadasu da mazan nasu sai su nemi saki.

Idan ka samu mata masu kyau halitta guda 10, sai ka samu 6 daga cikinsu sun taba yin aure fiye da sau daya.

  1. Mata Masu Illimi Mai Zurfi:

Su rukunin irin wadannan matan ba wai auren ne basa son zaman ba, babban matsalarsu shine basa son namijin da zai sa su ko ya hanasu. Wannan yasa koda sunyi aure suke kasa zama da mazan sai su fito.

Sai dai ga namijin da bazai takurasu ba zai sakar musu mara suyi abunda suke ganin shine dai-dai, to anan suna iya zama.

Domin akasarin irin wadannan matan za a samesu suna rike da wani matsayi na mukami a rayuwarsu. Ko kuma suna harkar kansu da basa son matsi ko takura.

  1. Mace Mai Tsananin Kishi:

Duk wata mace mai tsananin kishi bata iya zaman aure. Saboda a kullum tana son ta rika bibiyan abunda mijinta yake yi a gida da wajen gida.

Mata ne da suna iya yiwa mazajensu rashin mutunci a kowani lokaci a kuma ko ina.

Duk irin kauna da soyayyar da namiji yake yiwa mace mai zafin kishi dole ya hakura da ita muddin yana son yayi tsawon rai a duniya. Wannan yasa idan aka auresu dole ake rabuwa dasu.

  1. Matan Da Suka Saba Da Zina:

Duk macen data saba da zina yana da wahakar gaske ta iya zaman aure.

Kamar namijin daya saba da zina ne, da zai ajiye mata 12 idan anayi dole sai ya fita yayi wannan zinar, haka ita ma mace mazinaciya take. Hakurin saduwa dana miji guda ba sauyi bata saba da shi ba. Ita burinta duk namijin da yayi mata kawai ta nemeshi. Don haka aure zai iya takura mata a rayuwarta.

  1. Mata Masu Buri Na Musamman:

Akwai matan da suke da burin da suke fatan ganin sun cika a rayuwarsu. Irin wadannan matan burin nasu yana biyowa ne da wasu abubuwan da ba duk maza bane suke iya hakuri da basu hadin kai domin cimma su ba. Hakan yake sawa koda bayan auren idan miji ya nuna bayason abunda take so, sai ta gwammace rabuwa da shi maimakon jinginar da wannan burin nata data saka a gaba.

Akwai mata ‘yan kasuwa da suke da burin ganin sunfi Dangote kudi, irin wadannan matan a kullum suna cikin tafiye tafiye ko rashin zama ko kula da iyalansu. Mata masu irin wannan burin sun gwammace hakura da aure da a rusa musu shirinsu.

Haka nan akwai matan da suke da buri na siyasa. Suma mata ne da basu cika zaman aure ba ganin ba duk maza bane suke basu damar da zasu cimma wannan burin nasu.

Sai dai ba ana nufin cewa kwatakwata mata masu irin wadannan siffofin basa zaman aure ba. Tabbas akwai da yawansu masu zaman aure kuma lafiya da mazajensu. Don haka idan akace wasu, ba ana nufin duka ba.

Da fatan za a mana kyankyawan fahimta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button