Wasanni

Benzema ya bayyana ƙasar da yafi so ta lashe gasar Kofin Duniya

Gasar Cin Kofin Duniya 2022: Benzema ya bayyana ƙasar da yafi so ta lashe gasar Kofin Duniya.

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Karim Benzema ya dage cewa kasar Argentina karkashin jagorancin Lionel Messi tana cikin kyakkyawan yanayi na lashe gasar cin kofin duniya ta FIFA na bana a Qatar.

Benzema ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan kasar da aka fi so ta lashe kofin duniya a bana.

Argentina tana rukunin C a gasar cin kofin duniya ta 2022 kuma za ta kara da Poland da Mexico da kuma Saudi Arabia.

A ranar Litinin 21 ga watan Nuwamba ne za a fara gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2022 a filin wasa na Al Thumama lokacin da Senegal za ta kara da Netherlands a rukunin A.

Da yake magana a kan kasar da ya fi so ta lashe gasar cin kofin duniya, Benzema ya ce ta ESPN Argentina: “Mafi so? Kamar yadda na fada koyaushe, a kwallon kafa, babu wanda aka fi so. Amma na yi imani cewa Argentina tana cikin kyakkyawan lokaci.

“Kwagayya ce mai ban mamaki tare da ‘yan wasa kamar Messi, Di María. Babbar tawagar kasa ce

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button