Labarai

Tirkashi: Kotun Ribas ta gurfanar da wadanda ake zargin magoya bayan Atiku ne bisa laifin hada baki da tarukan da ba bisa ka’ida ba

Wata kotun majistare da ke zamanta a garin Fatakwal a jihar Ribas ta tasa keyar mutane sama da 20 a gidan gyaran hali na jihar.

An damke su ne dangane da wani taro da mambobin kungiyar goyon bayan Atiku a jihar suka yi.


Daga baya an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya bisa zargin hada baki da kungiyar asiri da kuma haduwa ba bisa ka’ida ba a gaban babban alkalin kotun, Collins Ali.


Sai dai Alkalin Kotun Mai shari’a Ali ya ki amincewa da bukatar belin da Lauyan ya gabatar wa wadanda ake zargin. Ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali tare da dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 22 ga Maris, 2023, domin a duba belinsu. Cikakkun bayanai daga baya…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu