Labarai

ASUU Ta Nemi Saka Dokar Hana Yaran Manyan Ƙasar Nan Zuwa Ƙasashen Waje Domin Karatu

ASUU Ta Nemi Saka Dokar Hana Yaran Manyan Ƙasar Nan Zuwa Ƙasashen Waje Domin Karatu

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi kira da a samar da kudirin doka da zai hana ‘ya’yan jami’an gwamnati Nijeriya da ke shiga makarantun ƙasashen waje dumin karatu.

Shugaban Jami’ar Neja Delta reshen Wilberforce Island na kungiyar Kingdom Tombra ne ya bayyana haka a wajen zanga-zangar hadin kan da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta shirya a ranar Talata a Yenagoa.

Ku tuna cewa kungiyar NLC ta fara zanga-zanga a fadin kasar domin nuna goyon bayanta ga kungiyar ASUU da sauran kungiyoyin da ke da alaka da harkar masana’antu a fadin kasar nan a jami’o’in gwamnati a Najeriya.

“Idan aka yi haka, za ta samar da ingantacciyar al’umma ta hanyar bunkasa manyan cibiyoyin ilimi da inganta kudade na tsarin jami’a a Najeriya.

“Wannan gwagwarmayar ba ta adawa da gwamnati ba ce, a’a ta bangaren ma’aikata da masu mulki ne kuma mun jajirce sosai

“Idan masu hannu da shuni suka je jami’a ko cibiya daya, ba na jin za a sake yajin aikin.

“Idan sun yi makaranta a nan kuma ‘ya’yansu suna nan za su nuna cikakken goyon baya ga tsarin jami’a da kuma manyan makarantun Najeriya,” in ji shi.

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne malaman jami’o’i mallakin gwamnati suka fara yajin aikin gama gari a fadin kasar, kan amincewa da tsarin bayyana gaskiya da rikon amana na jami’ar (UTAS) a matsayin tsarin biyan kudi a bangaren jami’ar.

Tun da farko, John Ndiomu, shugaban kungiyar NLC a Bayelsa ya bukaci gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan daftarin yarjejeniyar da aka sake tattaunawa tsakaninta da ASUU.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button