Labarai

PDP ba zata iya mulki ba kuma na fita Daga Jam’iyyar Inji Tsohon Ministan Neja Delta Godsday Orubebe.

DAGA :- Manuniya

Jam’iyyar PDP ba zata iya mulki ba a shekarar kuma na fita Daga Jam’iyyar Inji Tsohon Ministan Neja Delta Godsday Orubebe ya fice daga jam’iyyar.

Godsday Orubebe ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aika wa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata. Iyorchia Ayu.

Abin da wasikar take nufi shine , ya dauki matakin ne saboda jam’iyyar PDP ba ta shirya karbar mulki daga jam’iyya Mai mulki ba ta APC a zaɓen 2023 ba.

Abinda takardar wasiƙar take cewa, “Na rubuta ne domin in sanar da ku a hukumance cewa na fice daga Jam’iyyar (PDP). Ya bayyana hakane ga shugaban karamar hukumar Burutu, jihar Delta, A ranar 20 ga watan Yuni 2022.

“Nayi wannan wasiƙar ne dan na sanar da ku cewa na fita Daga Jam’iyyar PDP tun Daga matakin ward, Local Gvt, Jiha da ƙasa baki ɗaya.

“Lokacin da muka fadi zaben shugaban kasa a shekarar 2015 a cikin rudani, ko kadan, na yi imani cewa jam’iyyar za ta yi amfani da lokacin ‘yan adawa don sake yin dabarar kwace mulki da wuri.

“Dalilai da yawa da kuma akwia abubuwa da yawa da za a fada, amma saboda girmama jam’iyyar, na bar wasu labarai ba a bayyana su ba a wannan lokacin.

Imanina da tsattsarkan Najeriya bai girgiza ba, kuma zan ci gaba da yi mata aiki don ci gabanta da ci gabanta, ko da ta wata hanya ce.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button