Labarai

Wasu Mahara Sun Kashe Mutum 3 tare da Raunata 2 a Jihar Imo

Wasu ‘Yan Bindiga da ba’asan ko su waye ba Sun hallaka mutum 3 a jihar Imo.

Daga Manuniya

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo a ranar Lahadin da ta gabata ta tabbatarwa da manema labarai cewa mutane uku ne suka mutu sannan wasu biyu suka samu raunuka yayin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari tare da harbe wasu mutane da suke wani taro a Umuebele, Okporo a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo a ranar Alhamis din da ta gabata.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, Micheal Abattam, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Owerri babban birnin jihar.

A cewar ‘yan sandan, ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba sun zo ne a cikin Red Toyota Sienna ba tare da lambar rajista ba suka kai hari tare da harbe mutanen biyar sannan suka wuce da motar zuwa inda ba a sani ba.

‘Yan sandan sun ce: “Bayan rahoton da aka samu a ranar 16/6/2022 da misalin karfe 08:00pm, wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai da ke aiki a cikin wata mota kirar Toyota Sienna, ba tare da lamba ba, sun kai hari tare da harbe mutane biyar sannan suka tafi da wuri zuwa inda ba a sani ba a Umuebele Okporo. Orlu, Jihar Imo.

“Sakamakon haka, mutane uku sun mutu nan take yayin da wasu biyu suka samu muggan raunuka daban-daban na harsashi kuma an garzaya da su zuwa wani asibiti da ke kusa domin yi musu magani. Daga baya an gano gawarwakin kuma aka ajiye su a dakin ajiyar gawa.”

“A halin da ake ciki yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike, an kuma yi wa al’umma da muhallinsu kariya tare da karin jami’an tsaro. Bugu da kari, rundunar tana aiki tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro domin ganin an kama wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da fuskantar fushin doka,” in ji Rundunar ‘yan sandan.

Daga Manuniya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button