Labarai

Yan Arewa Mu Farka! Yan Kudu Sun Shirya Tsaf Dan Zaba Mana Wanda Suke so

Yan Arewa Mu Farka! Yan Kudu Sun Shirya Tsaf Dan Zaba Mana Wanda Sukeso a matsayin Shugaban ƙasar Nijeriya.

Daga:- MANUNIYA

A bin ciken ƙwaƙwafi da akayi an gano cewa ‘yan kudu suna da haɗin kan da ‘yan Arewa basu dashi akan zaɓen Shugaba na gari, Saboda dalilai da dama da suka faruwa a Arewa da Kudu a Nijeriya.

Kamar yanda ku ka sani cewa duk da wani ɗan ƙasa bashi da damar yin zaɓe har sai ya cika shekara 18 San nan kuma sai yana da Latin zaɓe.

Amma ‘yan Arewa basu da niyyar yin katin Zaɓe saboda ‘yan kudu sun shirya tsaf dan yin zaɓe, Yanzu haka a Kudun kome zaka yi sai kana da katin Zaɓe koda zaka shiga coci kayi ibada sai kana da katin Zaɓe.

wannan dalilin ne yasa kowa a Kudu indai yakai shekara 18 sai yaje anyi masa katin Zaɓe, Amma mu Arewa shiru lake ji sai kaga mutun ɗan 25 har zuwa sama amma bashi da katin zaɓe.

Wannan dalilin ke nunawa cewa mutanen kudu su zasu yi zaɓe kuma su zaɓi wanda suke so ya zama shugaba a Nijeriya, mutanen Arewa muna ganin cewa muna da yawa.

Amma yawan da mutanen Arewa muke da bashi da amfani saboda babu haɗin kai, ko da za’a sa doka akan katin zaɓe Arewa mu zamu fara karyata.

Zaku iyya kallon cikakken Bidiyon bayanin a nan ƙasa 👇👇👇👇👇

‘Yan Arewa mu farka akwai Babbar matsala.🖕🖕

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button