Labarai
Buhari ya jinji nawa Ramatu Aliyu ministan Abuja

Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya Taya minitan babban birnin tarayya Ramatu Tijjani Aliyu murnar ranar haihuwarta ta cika shekara 52.
Daga :- MANUNIYA

Buhari ya Taya Dr Ramat Tijjani Aliyu ƙaramar ministan Abuja da iyyalan ta murnar zaga yowar ranar haihuwar ta, ta cika shekara 52 a Duniya a 12 ga watan Yuni.
A saƙon Buhari, Mai taimakawa Shugaban ƙasa Muhammad Buhari harkokin yaɗa labarai ya bayyana a Ranar Lahadi a Abuja , Dr. Ramatu Tijjani Aliyu a matsayin ɗaya daga cikin Matan dake Burin Cigaban Nijeriya.
Ya ƙara da cewa Ministan Dr. Ramatu Tijjani Aliyu ke nuni da cewa mata a cikin harkokin siyasa da Cigaban ƙasa zasu bada gudun mawa sosai.