Album/EP

Abubuwa 7 da Bola Tinubu Ke Burin Yiwa ‘Yan Nijeriya

Abubuwa 7 da Bola Ahmed Tinubu Yake Da Burin Yiwa ‘Yan Nijeriya Idan Ya Gaji Shugaban ƙasa Muhammad Buhari a APC.

Bayan nasarar da ya samu a kwanan baya a zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ga jerin ajandoji guda bakwai na Asiwaju Bola Tinubu.

Tinubu, wanda ya samu kuri’u 1,271, ya doke wasu mutum 13 a zaben. Babban abokin hamayyarsa shine tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya samu kuri’u 316.

Burin nasa na gaje Buhari ya samu tasgaron ‘yan adawa daga wasu mukarrabansa da suka hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda ya samu kuri’u 235.

Ga jerin ajandojinsa ga kasar idan aka zabe shi a 2023 a cewar PM News.

Samar da shugabanci na sauyi mai kyau wanda zai hada kan ‘yan Najeriya baki daya kuma ya kai kasar ga cimma manufa da hangen nesa nagari.

Yin amfani da fasahar zamani don kawo sauyin tafiya daidai da zamani da habakar tattalin arzikin kasa.

Kirkirar yanayin da zai ba ‘yan ƙasa damar sakewa da yin mu’amala cikin ‘yanci a cikin kasa.
Kirkirar yanayin da zai ba ‘yan ƙasa damar sakewa da yin mu’amala cikin ‘yanci a cikin kasar.
Kawo babban ci gaban ababen more rayuwa ta hanyar gina muhimman ayyuka (sa’o’i 24 na samun wutar lantarki, hanyoyi, gadoji da dai sauransu) wadanda za su hada kasa tare da habaka ingancin rayuwa.

Gina tsarin da ke ba da daman karfafa kasuwancin cikin gida don habaka gasa mai kyau da gogayya da kasuwannin duniya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button