Album/EP

Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya ‘kada ku ƙyale PDP ta mayar da Najeriya gidan jiya’

Shugaban ƙasa Muhammad Buhar ya yi kira ga ‘yan Najeriya ‘kada ku ƙyale PDP ta mayar da Najeriya gidan jiya.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya su tabbata ba su bar jam’iyyar adawa ta PDP ta mayar da ƙasar gidan jiya ba.

Lokacin da yake jawabi a wurin zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasa na jam’iyyarsu ta APC, Buhari ya ce APC ta gyara Najeriya ta hanyar gudanar da ayyukan raya ƙasa.

“Wajibi ne mu zaɓi masu adalci ‘yan kishin ƙasa da ke da aƙidar haɗa kan ƙasarmu…don ciyar da ita gaba.

“Bai kamata mu ƙyale PDP ta mayar da Najeriya baya ba.”

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton PDP ba ta mayar da martani ba, wadda tuni ta zaɓi Atiku Abubakar a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a babban zaɓe na 2023.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button