Album/EP

Bola Ahmed Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani Na Jam’iyyar APC.

An bayyana tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

DAG MANUNIYA

Sanata Asiwaju na jihar  Legas ya samu rabin kuri’un da aka kada inda ya doke manyan abokan hamayyarsa, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan Koggi Yahaya Bello ,da Gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi.

Tin jiya da dare kimanin wakilai 2,322 daga sassan kasar nan ne suka mamaye dandalin Eagle Square da ke Abuja, domin zaben dan takarar jam’iyyar gabanin babban zaben 2023.

Har Tinubu, wanda ke rike da mukamin shugaban jam’iyyar na kasa, ya samu kuri’u 1,299, manyan abokan hamayyarsa, tsohon gwamnan jihar Ribas da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya samu kuri’u 292 da 216.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya samu kuri’u 140 yayin da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya samu kuri’u 42.

Daga cikin wadanda suka sayi fom din takara na Naira miliyan 100, an yi nasarar tantance 23 domin su shiga zaben fidda gwani.

A halin da ake ciki, Tinubu zai fafata da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, da sauran ‘yan takarar jam’iyyar domin neman babban mukami na siyasa a zaben 2023 mai zuwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button