Album/EP

Deliget din Jigawa ya yanki jiki ya fadi matacce a gurin zaɓen fidda gwani na APC a Abuja.

Deliget din Jigawa ya yanki jiki ya fadi matacce a gurin zaɓen fidda gwani na APC na ƙasa a Abuja.

Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaben fidda gwanin APC, jigo a jam’iyyar ya kwanta dama An ruwaito cewa, deliget daga jihar Jigawa ya yanki jiki ya fadi saboda bugun zuciya da safiyar yau dinnan Duk da cewa majiya ta tabbatar da faruwar lamarin, har yanzu ba a bayyana lokacin jana’iza ba tukuna

Gurin jana’izar Wanda ya mutu a gurin zaɓen fidda gwani na APC na ƙasa Yau a Abuja.

Abuja – Daya daga cikin wakilan jam’iyyar APC na Jigawa Alhaji Isah Baba Buji ya rasu yayin da yake wurin taron zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar a Abuja. Ya fadi ya mutu ne sakamakon bugun zuciya a safiyar ranar Talata a ofishin hulda da jama’a na jihar Jigawa da ke Abuja.
Marigayin dai shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Jigawa ta tsakiya, inji rahoton jaridar The Nation

DAGA MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button