Labarai

Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari Ya Tafi Ƙasar Spain

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi birnin Madrid na ƙasar Spain don wata ziyarar da ya kai Turai.

A yayin sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Femi Adesina ya fitar yace Buhari ya amsa gayyatar shugaba ƙasar Spain Pedro Sanchez kuma ya yi wannan tafiyar da ministocin Nijeriya guda biyar wanda suka haɗa da rakiyar ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Antoni Janar, Abubakar Malami (SAN).

Sannan sanarwar ta ce shugaban Najeriya zai kuma gana da shugaban gwamnatin Sifaniya, mai girma Sarki Felipe na 5.

DAGA :- MANUNIYA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button